Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba ya fushi kuma bai kullaci duk wani mai kishin kasar nan da ke ganin gwamnatin sa ta ba tabuka komai ba.
Da ya ke karanta jawabin sa ga ’yan Najeriya a ranar Juma’a, ranar farkon sabuwar shekarar 2021, Buhariya ce duk wani mai kishin kasar nan mai ganin cewa mulkin sa bai tabuka wani abin a zo a gani ba, ya san ya na yi ne saboda kishi da kuma dokin ya ga kasar nan ta gyaru sosai.
Sai dai kuma ya ce duk da haka, ba zai daina tuna wa jama’a cewa su yi wa gwamnatin sa adalci ta hanyar tuna halin da kasar nan ke ciki a lokacin da ya karbi mulki a 2015.
“Ni dai a matsayi na na Shugaban Kasa, na yi maku alkawarin ci gaba da yin bakin kokari na, kamar yaddda na ke kan yi. Zan ci gaba da gudanar da mulki na ba tare da fargabar wani ko nuna wa wasu fifiko ba.
“Saboda haka ina kira da gayyatar kowane dan kasa ya tashi ya nuna kishin kasar nan da aiki tukuru tamkar ya na yin gasa da ni.
Sannan kuma ya ce gwamnatin za ta kara dauka majayin goya dimbin matasa a baya, domin samar masu ayyuakn dogaro ta hanyar samun aiki da inganta hanyoyi da dabarun kirkirar kananan sana’o’i.
Buhari ya jaddada cewa shekarar 2021 shekara ce da za mu kara karfafa wa ’yan Najeriya fatan da su ke da shin a ganin an samu Najeriya ta zama kasa kasaitacciya.
A cewar sa, gwamnatin sa za ta kara karafa yaki kudirorin ta ko ajandojin ta guda uku, wato tsaro, yaki da rashawa da kuma inganta tattalin arziki.