Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an kama bakin-haure har 1,375 a tsawon lokacin da kan iyakokin Najeriya su ka kasance a kulle.
An kama bakin-hauren a tsakanin watan Agusta 2019 zuwa 17 Ga Disamba 2020.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Lagos ranar Litinin, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Ministan ya kara da cewa an kwace buhunan shinkafa 157,511, wadanda duk manyan buhuna ne masu nauyin kilogiram 50.
An kuma kwace buhunan takin zamani 10,447 samfurin NPL da ministan y ace ana amfani da su ne ana hada bom na gargajiya.
An kuma kwace jarka 18,630 ta man girki.
Lai ya kiyasta kudaden kayan da aka kama za su kai naira bilyan 12.362.
Ya ce an kama kayan bayan an kaddamar da shirin tsare kan iyakokin Najeriya a dukkan yankunan ksar nan.
Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro ya shirya atisayen domin bunkasa tattalin arziki da kuma tsare kan iyakokin Najeriya.
Shirin ya kunshi gamayyar jami’an kwastan, jami’an shige-da-fice, sojojin Najeriya da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an leken asiri.
An dai bude kan iyakokin Najeriya a ranar 16 Ga Disamba bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni.
Kan iyakokin da aka bude sun hada da Seme, Illela, Maigatari da Mfun.
Ya ce an samu nasarar dakile shigo da muggan makamai, muggan kwayoyi da sauran haramtattun kayan da Najeriya ta hana yin fasa-kwaurin su.
Sannan kuma ya ce an samau nasarar bunkasa tattalin arziki da kuma inganta tsaro da bunkasa harkokin noma a cikin kasar nan.
Discussion about this post