Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutum biyu dukkan su kuma ma’aikatan Hukumar Wutar antarki ta Yola (YEDC) bisa zargin yin lalata da matar sa.
Wani mijin da ya yi zarginan yi lalata da matar sa ne ya garzaya ofishin ’yan sanda ya kai kara.
Har ila yau wadanda aka kama din su na jagorancin ibada a wani coci-coci.
Otinjele limami ne a wani coci mai suna mai suna Liberty International Gospel Centre a Yola Jihar Adamawa.
Juliana kuma mai wa’azi ce a wani cocin daban.
Har zuwa yau ana tsare da su a bangaren CID a Yola.
Ita dai Juliana Daniel, mata ce ga Eli Daniel, wani jami’i a Ma’aikatar Makamashi ta Tarayya, Abuja.
An yi zargin cewa ita matar Daniel ta yi aiki a karkashin Otinjele, a lokacin ya na Manajan Kasuwancin Hukumar Lantarkin Yola.
An ce a can ne su ka rika tabka lalata son ran su.
Daniel ya shaida wa wakilin mu cewa ya auri matar sa tun cikin 2002 a Numan, kuma su na da yara biyar.
“A cikin yaran nata guda biyar, na tabbatar yara biyu ba ni na yi cikin su ba. Wani mai suna Ebenezer ne ya yi cikin amma ta nuna kamar ni na yi cikin.”
“Na samar mata aiki a cikin 2016 a Yola, a ofishin hukumar hasken lantarki, inda ta ke aiki a karkashin Fasto Ebenezer. To a can ne su ka rika balle bahallatsar su har ya yi mata ciki sau biyu.
“Tun mata ta na bin Ebenezer su na lalata a wani wuri, har ta kai abin ya zame masu jiki su na yi a cikin gida na, a kan gado na a Mbamba.
“Idan Ebenezer ya zo kwartanci gida na, sai su aiki yara su sayo wani abu can a wani wuri mai nisa. Idan lokacin karatu ne kuma, sai yara sun tafi makaranta ya ke zuwa.”
“Ranar 15 Ga Satumba, 2016 Ebenezer Otinjele ya dauki mata su ka tafi shakatawa a Jalingo. Haka ta tafi ta bar karamin yaro a hannun yarinya mai shekaru 12. Rashin lafiya ta kama yaron, har ya mutu ba ta dawo ba.”
Ya ce matar sa ta haifi yara biyu da Otinjile tabbas.
An dai kama su ne an tsare bayan da lauyan Daniel mai suna Abdul Sule ya rubuta wa Kwamishinan ‘Yan Sanda takardar korafi.
PREMIUM TIMES ta kasa jin ta bakin matar da ke kulle da kuma Ebenezer Otinjile saboda su na tsare a hannun jami’an tsaro.
Kakakin ‘yan sandan Adamawa ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, kuma ya ce su na bincike.
Discussion about this post