Babu tsarin karba-karba ba a APC – Shekarau

0

Tsohon gwmnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta da wani tsarin karba-karba a kundin dokokin ta.

Shekarau ya ce maimakon a rika maganar karba-karba, a maida a hankali wajen zabo wanda ya dace ne maimakon dole-dole sai an canja yaki idan wa’adin wanda yake kai ya cika.

” Bari in gaya muku ku sani yau, babu wani wuri a kundin dokokin APC da aka yi maganar karba-karba. Ina ganin maganan karba-karba na can a tsarin PDP ne.

” Abinda muke so shine shugabanci nagari, wanda kowa na shi ne. Shugabancin da za a gyara kasa a kawo cigaba.

Bayan haka Shekarau ya ce akwai kyakkyawar fahimta a tsakinin shi da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da tsohon Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso.

” Tun ina babban sakatare a gwamnatin Kano, Ganduje na Kwamishina muke tare lafiya lau sumul. Haka shima Kwankwaso, ban taba bari banbancin siyasa dake tsakanin mu ya raba mu ba. Siyasa da ban zumuncin da ban.

Sanata Shekarau yace ko a lokacin da ya canja sheka daga PDP ya koma APC, yayi haka ne ba don dawowar Kwankwaso jam’iyyar ba, shugabancin jam’iyyar ce bata yi masa ba. Haka kuma ko a lokacin da yake jam’iyyar APC

Share.

game da Author