Ba wanda ya isa ya kori Fulani makiyaya daga Jihar Oyo – Gwamna Makinde

0

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya nuna goyon bayan sa ga Fulani makiyaya, wadanda ba su tayar da zaune tsaye a jihar Oyo.

Makinde ya ce duk makiyayin da ke zaune lafiya da jama’a, ya na da ’yancin zama kowace shiyya a kasar nan, kamar yadda dokar kasa ta ba kowane dan Najeriya ’yanci.

Makinde ya ce bayar da wa’adi ga makiyaya su tashi daga wani wuri an tauye masu hakki da ‘yancin su kamar yadda kowane dan Najeriya ke da irin wannan ’yancin.

Da ya ke magana kai tsaye a ranar Laraba, Makinde na Oyo ya ce mabarnata masu garkuwa da kisa su ne ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ya ce su kuma masu kiwon shanu, daban su ke, abinda kawai su ka sa a gaba shi ne kiwon shanun su da kuma yawon neman inda ciyawar da dabbobin su za su ci.

Ya ce duk wani da ya bai wa makiyaya wa’adin ficewa daga jihar sa, to ya tauye masu hakki ne kawai.

“Ba wai ba mu san akwai matsalolin da aka rika fuskanta ba, kuma ana fuskanta har yanzu. Zaman lafiyar da aka kulla tsakanin makiyaya da manoman Oke-Ogun na samun barazana yanzu haka.

“ Wadansu tsirarun da ba a karkashin hukuma su ke ba, sun fara daukar doka a hannun su. Wannan barna ce da karambani su ke yi, kuma ba da irin wannan hanyar za a iya neman wani muradi da Yarabawa ke nema a cikin kasa ba.”

“Bari na kara furtawa da babbar murya. Ba za mu zura ido mu na ganin ana yi wa rayuwar duk wani mazaunin Jihar Oyo cikin lumana na fuskantar barazana a rayuwar sa ba, a gidan sa ko a gonar sa ba ko a wurin kasuwancin sa.

“Mu na sane da wasu mutane da su ka fara raba takardu su na sanar da wasu mazauna yankin su wai su fice su bar masu kasa. Ba za mu taba amincewa da wannan ba ko kadan.”

Makinde ya ce Dokar Najeriya ta 1999 Sashe na 41(1), ya bai wa kowane dan Najeriya da ke zaune da mutane lafiya dama da ‘yancin yin rayuwar sa a duk inda ya ke so a cikin kasar nan.

“Don haka mu ma a nan Jihar Oyo mun kudiri kare wa kowa wannan dama da dokar kasa ta ba shi.”

Wannan gargadi na Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya zo ne kwanaki kadan bayan da gwamna Akeredolu na Ondo ya bai wa Fulani Makiyaya wa’adin kwanaki bakwai su fice daga dazukan jihar Ondo.

Akeredolu ya yi kukan cewa shekara da shekaru an kasa samun zaman lafiya, saboda rikice-rikice da manoma da kuma garkuwa da mutane da ake zargin wasu batagarin Fulani na yi.

To can kuma an samu zaman dardar a jihar Oyo yayin da wani mai suna Sunday Igboho, mai rajin neman kafa kasar Yarabawa zalla, wato ‘Yoruba Nation’, ya yi sanarwar bada wa’adin ficewa ga Fulanin da ke zaune a Iparapa da ke yankin Igangan na jihar Oyo.

Ana ganin wannan ne ya sa Gwamna Makinde fitowa ya yi gargadin a daina karambanin kowar wata kabila daga jihar Oyo.

Sai dai kuma Sarkin Fulanin Jihar Oyo Saliu Abdulkadir, ya ce ba Fulani ba ne ke haddasa garkuwa a yankin, domin shi ma ana kama mutanen sa ana yin garkuwar da su.

Share.

game da Author