Shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa babu sauran wani uziri ko togaciya da rundunar sojan Najeriya za ta bayar, domin an ba su wadatattu kuma isassun makudan kudaden magance matsalar Boko Haram a cikin 2021.
Ndume ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun samu duk wata bukatar da su ka nema a biya masu ta fannin sayen manyan makamai da lodin sauran kayan artabu, domin magance Boko Haram da ’yan bindiga a Najeriya.
“A yanzu dai sojojin Najeriya sun samu abin da duk su ke bukata.” Inji Ndume.
Wannan bayani na Sanata Ndume ya zo ne kusan mako daya bayan Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa, “sojoji za su kunyata Boko Haram cikin 2021.”
Idan ba a manta ba, kusan karshen 2020, Buratai ya fito baro-baro ya ce, “akwai yiwuwar a kara shekara 20 nan gaba ana fama da Boko Haram a kasar nan.”
Da ya ke tattaunawa da PREMIU TIMES, Ndume ya kara cewa gwamntin tarayya ta amince da dukkan bukatun da mahukuntan tsaro na soja su ka mika domin magance ta’addanci da ’yan bindiga a kasar nan.
“A wannan shekarar shugabannin sojoji cewa su ka yi su za a damka wa kudade a hannun su domin su sayo kayan da su ka ce ya kamata a sayo. Kuma hakan aka amince. Har ma an sa hannu cewa su za a damka wa kudaden.” Inji Sanata Ndume.
“To yanzu dai ga kudi a hannun su. A gaskiyar magana ma a cikin wannan kasafin kudaden, Majalisa cewa ta yi a gaggauta damka wa sojoji dukkan makudan kudaden da su ka bukata daga nan zuwa Maris. An yi haka ne domin su samu damar sayo manyan makaman da su ke bukata.
“Kuma duk wani abin da za a yi wa sojoji masu yaki domin a kara mau kishi da kuzari da jajircewa, to akwai shi cikin kasafin 2021.
“Kasafin Kudin Sojoji na 2021 tun daga albashi da komai, ya kai naira bilyan 500.
” Shekarar da ta gabata naira bilyan 75 aka kashe wa Operation Lafiya Dole kadai. Amma wannan shekarar shugabannin sojojin sun yi korafi, sai mu ka yi masu kari zuwa naira bilyan 100.’’ Inji Ndume.