Ba a tabbatar ko Uwargidan El-Zakzaky ta kamu da Korona ba – Hukumar gidajen Yari

0

Duk da tabbatar da kamuwa da Korona da daya daga cikin ‘ya’yan Zeenat El-Zakzaky dake tsare a Kaduna yayi Hukumar gidajen yari ta kasa, a kaduna ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu tabbacin ko Zeenat ta kamu da cutar ba.

Daya daga cikin ‘ya’yan uwargidan El-Zakzaky ya ce mahaifiyar sa dake tsare ta kamu da Korona bayan gwajin da likitoci suka yi mata a inda take tsare.

” Likitoci dake kula da mahaifiyata sun yi mata gwaji a lokacin da suka je duba su na duk mako. Ta shaida musu tana jin kasala a jikin ta da gabobinta, bata jin kamshin kuma zazzabi ya rufe ta. Daga nana sai suka dibi samfurinta sannan suka yi mata wasu gwaje-gwaje.

” Bayan sun dawo da sakamakon gwajin sai aka ga ta kamu da Korona.”

Sai dai kuma Kontirolan firsin din Kaduna ya shaida cewa ba a sanar dashi sakamaon gwajin da aka yi wa uwargidan El-Zakzaky ba, saboda haka bashi da masaniya cewa wai ta kamu da korona ko bata kamu da cutar ba.

” Tun bayan gwajin da aka yi mata kwanaki shida da suka wuce aka killace ta zuwa sakamakon gwajin ya fito.

Dan Zeenat ya koka cewa ba a ba mahaifiyar sa kula yadda ya kamata a inda take tsare.

Share.

game da Author