Atiku ya saida hannayen jarin sa a kamfanin Intels, ya ce Buhari ya sa shi a gaba

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya sayar da dukkan hannayen jarin sa a kamfanin Intels.

Atiku wanda ya fara sayar da hannayen jarin a hankula tun shekarun baya, ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda tun farkon hawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari aka dauki tsauraran matakan sai an karya shi.

Wata sanarwa da kakakin yada labarai na Atiku, wato Paul Ibe ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya ce ya yanke shawarar sayar da hannayen jarin sa kakaf a kamfanin Intels, saboda gwamnatin Buhari ta rugurguza tattalin arzikin Najeriya.

“Tunanin ya zo ne saboda tun shekaru biyar da su ka gabata Gwamnati ta rika bugun-kirjin sai ta karya harkar kasuwancin Intels, kamfanin da ya dauki dubban ma’aikata aiki. Kuma duk wannan karya kamfanin da ta yi, saboda dalilai ne kawai na siyasa.”

Atiku wanda ya yi mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007, kuma ya yi takarar shugaban kasa tare da Buhari cikin 2019, ya ce kamata ya yi a ce batun siyasa badan, haka batun harkar kasuwanci kuma ita ma daban.

Atiku ya ce ya karkata kudin hannayen jarin sa daga Intels zuwa wasu harkokin kasuwancin da za su samar wa dimbin jama’a ayyukan yi a kasar nan.

Asalin Sabani Tsakanin Intes Na Atiku Da Gwamnatin Najeriya:

A rnar 4 GA Satumba, 2020 ce PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta soke dadaddiyar kwangilar da ta ke yi da Intels, kamfanin Atiku.

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa ta soke dadaddiyar kwangilar da hukumar ke aiwatarwa tsakanin ta da Intels Nigeria Limited, INL, mallakin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Cikin wata takardar da aka buga Mai dauke da bayanai da labaran da suka kunshi harkokin tashoshin jiragen ruwa a Lagos, a ranar 1 Ga Satumba, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, wato NPA ta ce an soke kwangilar tun a ranar 1 Ga Satumba din.

Sanarwar ta kuma umarci dukkan masu jiragen ruwa su daina mu’amala kai-tsaye da Intels, su rika yi a ofisoshin NPA da ke Tashoshin Jiragen Ruwa na Lagos.

PREMIUM TIMES HAUSA ta samu kwafen takardar, wadda Shugaban Kula da Wuraren Ajiyar Jiragen Ruwa, Daniel Hosea ya sa wa hannu.

“Daga yanzu duk wani zirga-zirgar da wani jirgin ruwa zai yi daga kowace tasha dole a kai rahoto da neman izni tashi da tsayawa a Ofishin Babban Mai Kula da Wuraren Tsayawar Jirage. A can za bada fam a cika dangane da duk wani motsin da kowane jirgin ruwa ya yi.” Haka sanarwar ta bayyana.

NOAI Da ATIKU: Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa

An shafe shekaru tun bayan hawan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Tun a cikin watan Yuni, 2017 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cikakken labarin yadda rikici ya tirnike tsakanin NPAda Intels, kamfanin da Atiku ke da babban hannun jari a cikin sa.

An kafa Intels shekaru sama da 30 da suka gabata. Atiku Abubakar da wani Baturen kasar Italy ne suka kafa kamfanin. Sunan Baturen Gabriele Volpi. Wannan Bature kuma ya na da takardar zama dan Najeriya.

Cikin watan Afrilu na 2017, Shugaba Buhari ya amince da wata shawara da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ba shi a rubuce, cewa a karya lagon karfin ikon da kamfanin Atiku ke da shi wajen aikin kwangilar karbar kudaden kamasho ga gwamnati da Intels ke yi a kan duk wani babban jirgin daukar jigilar kayayyaki a tashoshin ruwan Najeriya.

Cikin Satumba, 27, 2017, Malami ya sake rubuta wa Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala Usman wasikar cewa ya na umartar ta da ta soke kwangilar dadaddiyar yarjejeniyar aikin kula da karbar kudaden kamasho da kamfanin Intels ke wa jiragen ruwa a madadin Gwamnatin Tarayya.

Malami duk a cikin wasikar ya shaida wa Hadiza Bala a cikin wasikar cewa Buhari ya amince kuma ya yarda cewa kwangilar haramtacciya ce.

Malami ya tsaya kai da fata cewa kwangilar wadda kamfanin Intels ya shafe shekara 17 ya na karar kudaden shigaa tashoshin jiragen ruwa a madadin Najeriya, haramtacciya ce.

Malami ya ce babu wani dalili da Intels ba zai rika zuba kudaden da ya karba a Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya ba, wato TSA.

Tunda an kirkiro TSA, ba a bukatar Intels ya ci gaba da yi wa gwamnati aikin karbar mata kudaden haraji kenan.

A na shi bangaren, kamfanin Intels ya ki amincewa da soke yarjejeniyar kwangilar da Najeriya ta dade ta na yi da Intels din.

Intels ya ce NPA ta soke kwangilar ba tare da gayyatar sa an zauna an tattauna ba.

Cikin 2019, Intels ya ce NPA ba ya bin sa bashin ko sisi, shi Intels din ya na bin NPA bashi ya kai na dala milyan 750.

Duk da Intels ya nuna ci gaba da aiki, domin gudun kada rashin-jituwa ya shafi har da dimbin mutanen da ke aiki a karkashin Intels din.

Sai dai wata sabuwa ta sake tashi, a ranar Alhamis PREMIUM TIMES ta gano cewa an yi watsi da batun Intels a harkokin kula da jiragen ruwa.

Yayin da wata majiya ta ce yarjejeniyar aikin kula da jiragen ruwa din ta kare, ana kokarin sabunta ta ne, tare da gindaya wasu sabbin sharudda.

Majiyar ta ce za a buga neman duk wani kamfani mai sha’awar so ya yi wannan aiki. Kenan shi ma Intels sai ya sake aikawa da kokon-bara kenan.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na NPA, Adams Jatto, wanda ya ce ba zai iya magana ba, saboda ya dauki hutu, ya na gida

Share.

game da Author