A ranar Juma’a ne masarautar Zazzau ta fada cikin jimamin rashin wasu daga cikin ‘ya’yanta Iyan Zazzau Bashar Aminu da Talban Zazzau Abdulkadir Iya-Pate.
Marigayi Iya ya rasu a wani asibiti dake jihar Legas.
An gudanar da jana’izan su bayan sallar Juma’a a babban masallacin juma’a dake Zariya.
Idan ba a manta ba, har Iya ya rasu ya na kalubalantar nadin Ahmed Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yayi in da ya ce shine ya fi dacewa ya mulki Zazzagawa bayan rasuwar Maimartaba Shehu Idris.
Yayi ce El-Rufai ya saba dokar nadin sabon sarki na masarautar Zazzau wajen nadin Ambasada Ahmed Bamalli, Sarkin Zazzau bayan rasuwar Sarki Shehu Idris.
Ya kai kara kotu a watan Oktoba, kuma ba a kai ga yanke hukunci ba Allah ya yi masa cikawa.
Iya ya ce shine ya fi cancanta ya zama sarkin Zazzau ba Ahmed Bamalli ba.
Discussion about this post