An yi garkuwa da yara 6 ‘yan gida daya a jihar Zamfara – Rundunara ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa mahara sun yi garkuwa da mutum bakwai a kauyen Kadauri dake karamar hukumar Maru.

Maharan sun far wa kauyen ranar Juma’a da safe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Shehu Mohammed ya tabbatar da uakuwar lamarin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a garin Gusau.

Mohammed ya yi kira ga mazauna kauyen Kadauri da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kamo mutanen da suka aikata haka a kauyen.

Bayan haka Sani Gyare mahaifin yara shida din da aka sace a gida daya ya ce maharan sun so su yi garkuwa da shi ne amma da ba su same shi ba suka yi awon gaba da ‘ya’yan sa shida.

” Da maharan suka shigo kauyen sun nufi gidana ne kai tsaye inda bayan sun neme ni ba su ganni ba sai suka kwashi ‘ya’ya na shida suka hada da dan abokina kuma makwabcina Alhaji Sani Yellow.

Share.

game da Author