Masu hada-hada kasuwannin Kantin Kwari, Kofar Wambai da Sabon Gari a Kano sun shiga cikin ruɗani da jimami, sakamakon yin garkuwa da wasu abokan kasuwancin su da aka yi garkuwa da su, su 27 a Okene, Jihar Kogi.
Lamarin ya faru ranar Lahadi a kan hanyar su ta zuwa garin Aba a jihar Abia domin sayo kayan bulawus da yadika.
Kakakin Ƴan Kasuwar Kwari, Mansur Haruna ya babbatar da faruwar lamarin, amma kuma ya ce ba dukkan matafiyan 27 ne ƴan Kantin Kwari ba.
“Wasu matafiyan ‘yan Kasuwar Kofar Wambai ne, wasu kuma daga kasuwar Sabon Gari duk su ka yi kwamba a mota daya su ka dunguma da niyyar tafiya Aba safarar kaya.
Haruna ya shaida wa Daily Nigerian cewa shugabannin kasuwar sun roki a dukufa da addu’a, inda runi har kwamitin yin addu’o’i a masallatai da gidaje aka kafa, domin Allah ya kubutar da ‘yan kasuwar.
Ya ce yawancin matafiyan duk wadanda jarin su bai wuce naira 400,000 ba ne. daga nan sai ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Gabduje na Jihar Kano ya sa baki a samu kubutar da su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta samu labarin yadda a kasuwannin ake cikin hali damuwa da jimami kan matsalar garkuwa da mutane a Arewa, musamman yadda abin ya shafi Kano a yanzu cikin halin bazata.
“Abin takaicin yawancin su fa jarin su bai wuce naira 400,000 ba kowanen su. To irin wadannan ya ka ke jin za su iya hada kudin fansar kan su?”
Wani dan kasuwar Kantin Kwari mai suna Garba Lawan, ya bayyana cewa ana tattaunawa tsakanin iyalan wadanda aka yi garkuwar da su, inda wadanda su ka kama su din ke neman kudin fansa har naira milyan 45 kan kowane mutum daya.
Sai dai kuma ya kara da cewa amma a yanzu su na bukatar a biya su naira milyan 27 domin su saki matafiyan su 27 baki daya.
Discussion about this post