An sace shugaban gidan Yari a hanyar Birnin Gwari-Kaduna a jajibarin 2021

0

Kakakin rundunar hukumar gidajen Yari na Kaduna Amodu Wadai ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun sace shugaban gidan yarin da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari, Saidu Sajo, a hanyar sa ta dawowa garin Kaduna ranar Alhamis.

Wadai ya ce an sace Sajo da misalin karfe biyun rana ne domin a lokacin suka samu labarin dauke shi da akayi.

Shi dai Sajo yana hanyar dawowa ga iyalan sa ne daga Birnin Gwari inda a can ne ya ke aiki zuwa Kaduna domin hutun sabuwar shekara, sai dai bai samu ya kai ga iyalan na sa ba, wuf masu garkuwa sun dauke shi a hanya.

Har yanzu babu labarin ko maharan sun tuntubi iyalan Sajo domin bayyana ko nawa za su biya su fanshi dan uwansu.

Share.

game da Author