Abinda ya fi dacewa ga wanda ya kamu kuma ya warke daga Korona shine ya yi ta Hamdala ga Allah – Obasanjo

0

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi duk wanda ya taba kamuwa da Korona sannan Allah ya bashi lafiyaya tattara kayan sa ya koma ga Allah.

” Duk wanda ya ga wannan shekara ta 2021, dole ya koma yayi nadama ya tattara hankalin sa wuri daya ya koma ga Allah kacokan ganin irin lafta-laftan ramukan da Allah ya sa ya tsallake su a 2020 har ya iya ganin 2021.

” Ba ga Najeriya ba ko Afrika ba, duk duniya an fada cikin tsananin fargaba a 2020. Dole mu daga hannayen mu bibbiyu mu godewa Allah kan tsallakar da mu wannan shekara har muka iya ganin shekarar 2021.

Obasanjo ya yi wadannan kalamai ne a jawabin da yayi a coci wajen bukin murnar shiga shekarar 2021.

Share.

game da Author