Kungiyar Masu Casar Shinkafa ’Yar Hausa a Najeriya (RPAN), ta yi kira ga gwamnatin tarayya cewa ta tashi tsaye haikan wajen tsaurara hukunci mai tsanani kan masu shigo da shinkafar sumogal daga kasashen waje.
Babban Daraktan RPAN, kungiyar da aka fi sani da Rice Procession Association of Nigeria, Andy Ekwelem ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya yi zantawar a ranar Asabar, dangane da yadda ake kara samun yawaitar shigo da shinkafa ta hanyar sumogal a cikin kasar nan.
Ekwelem ya kara da cewa idan har gwamnatin ba ta daukar kwakkwaran hukunci a kan masu sumogal din shinkafa daga waje, to dukkan masa’antun casar shinkafa na kasar nan durkushewa za su yi.
Ya ce matsawar aka bari su ka durkushe kuwa, to wadanda za su rasa aikin yi a kasar nan su na da yawan gaske.
Daga nan ya kara da cewa shigowar gwamnatin nan a yanzu a harkar shinkafa, daga noman ta zuwa sheke ta da casar ta zuwa dura ta a buhu, akalla ta samar wa mutum milyan 13 aikin yi.
Ya kara da yin nunin cewa idan masu sumogal su ka ci karfin noman shinkafa a kasar nan, to za a shiga mawuyacin halin kuncin rayuwa, musamman wadanda za su rasa ayyukan su sakamakon rufe masana’antun casar shinkafa, a yanayin da ake ciki na korana.
Ya ce masu sumogal din shinkafa sun farfado bayan da gwamnatin tarayya ta sake bude kan iyakokin kasar nan.
“Yanzu haka shinkafar sumogal daga kasashen waje ta cika kasuwannin kasar nan.” Inji Ekwelem.
“Mun sha fada ba sau daya ko sau biyu ba, cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta rika zartas da tsauraran hukunci a kan masu shigo da shinkafar sumogal accikin kasar nan. Saboda shinkafa ce abu na farko a jerin sunayen kayayyakin ba Babban Bankin Najeriya, CBN ya haramta shigo da su.
“Duk wata shinkafar da ka gani a cikin kasar nan, a kantina, a kasuwanni, ko a cikin gidajen su, to idan dai ba a kasar nan aka noma ta ba, to ku tabbatar cewa shinkafar sumogal ce.” Inji shi.