A karo na biyu a jere mahara sun sake afkawa mutanen Kuregu, Wusasa Zariya, sun sace mutum biyu

0

Idan ba a manta a makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka yi garkuwa da wazirin Wusasa Mohammed Aliyu dake unguwar Kuregu a Wusasa Zariya.

Mohammed wanda farfesa ne yana aiki a sashen koyar da ayyukan noma a jami’ar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi.

Daya daga cikin ‘ya’yan sa mai suna Usman Mohammed ya bayyana wa manema labarai cewa maharan sun harbi yayyin sa biyu inda nan take daya mai suna Abdulaziz ya mutu, dayan kuma Abubakar Kabir na kwance a asibiti a lokacin.

Wani makusancin iyalan farfesa Mohammed ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa maharan sun bukaci a biya miliyan 20 kudin fansar farfesa Aliyu.

Mutanen Kuregu ba su warware daga jimamin wannan abu ba sai kuma kawai a cikin daren ranar Asabar wato da safiyar Lahadi wasu maharan suka sake diran wa garin.

Maharan sun yi garkuwa da Sule Iliya da Japheth Yakubu.

Mai unguwar Kuregu Ahmed Amfani ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA da aka bukaci karin bayani game da wannan hari da aka kai unguwar cewa, bayan sace mutane biyu da maharan suka yi sun kashe wani dattijo wanda dan uwan daya daga cikin wanda aka yi garkuwa da shi ne, Japhet Yakubu.

” Tun a cikin dare na fara jin karar harbin bindiga, hakan ya sa na kira jami’an tsaro maza-maza su kawo mana dauki. Daga nan ne fa sojoji suka zo daga barikin Basawa suka fara musayar wuta da maharan.

Amfani ya ce am fafata da wasu ‘yan bijilante dake aiki a unguwar a lokacin da mahara suka iso.

A tattaunawa da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA mai unguwan Wusasa ta Tsakiya Abass Hassan shime ya tabbatar da aukuwar wannan mummunar al’amari yana mai cewa akalla mutum uku ne maharan suka kashe a batakashin da suka yi da jami’an tsaro da kuma yan bijilantin garin.

Sai dai PREMIUM TIMES HAUSA ba za ta iya tabbatar da haka ba a dalilin rashin ganin gawarwakin keke-da-keke.

Sarkin Wusasa Malam Isiyaku Yusufu ya zargi maharan da ke shawagi a dazukan dake kewaye da garin da aikata wannan mummnar abu.

A karshe basaraken ya mika godiyarsa ga sojojin barikin Basawa na gaggawar kawo wa mutanen kuregu dauki a lokacin da maharan suka afka musu.

Ko da PREMIUM TIMES HAUSA ta ziyarci gidajen wadanda aka yi garkuwa da ‘yan uwan su ta tarad da mutane wato’ yan uwa da abokan arziki sun yi tsaitsaye suna yi wa juna jajen abinda ya faru.

Har yanzu dai maharan basu tuntubi yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su ba.

Share.

game da Author