A bayyana wa duniya sakamakon binciken Magu –Cibiyar HEDA

0

Wata mai kungiya mai suna HEDA, ta zargi gwamnatin tarayya cewa babu wani zargin cin hanci da rashawa kan tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu sai bi-ta-da-kulli kawai aka yi masa.

HEDA ta ce ganin yadda aka kammala binciken sa, tuni tsawon wata da watanni, amma har yau an ki bayyana wa duniya laifin Magu, hakan ya zubar da kima da mutuncin wannan gwamnati a fannin yaki da cin hanci da rashawa.

A cikin wata wasika da ta aikwa wa Shugaba Muhammadu Buhari, cibiyar a matsayin ta na kungiyar da ke fafutikar ganin an kawar da cin hanci da rashawa a duniya, ta damu kwarai dangane da yadda aka yi amfami da kitimirmirar siyasa aka cire Magu ta hanyar kakaba masa tuggu da sharri.

Ta ce kin fitar da sakamakon binciken Magu domin duniya ta yi alkalancin zargin da aka yi masa, hakan ya tabbatar da cewa ba-ta-da-kulli ne kawai da tuggun ‘yan siyasa aka shirya wa Magu.

HEDA ta ci gaba da cewa rashin fitar da sakamakon binciken Magu ya kara zama dalilin da ya sa kungiyar TI ta kara danna Najeriya cikin zurfin ramin kasashen da cin hanci, rashawa da wawurar kudaden gwamnati su ka yi katutu.

Mutum hudu ne su ka sa wa wasikar korafin hannu, kuma su ka aika wa Shugaba Muhammadu Buhari. Sun kada da Olanrewaju Suraju, Simon Taylor, Lucas Manes da kuma Nicholas Hildyard.

HEDA ta nuna wa Buhari cewa ba fa mutuncin gwamnatin sa ba ce, wadda ke ikirarin yaki da cin hanci da rashawa a ce watanni bakwai tun bayan kafa wa Magu Kwamitin Ayo Salami, a ce har yau ba a itar da sakamakon binciken zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa ba.

Cibiyar ta ce tuni jama’a ke ta zargin cewa kawai dai ganin bayan kyakkayawan ayyukan da Magu ya yi wasu ‘yan-ta-kife su ka yi, wadanda su ka zubar wa Gwamnatin Buhari mutunci, daraja da karsashin kima.

HEDA ta ce ai tilas duniya ta cika da mamaki, domin wata da watanni bayan kammala binciken Magu da aka dauko ana yi kamar tashin guguwa, to an kammala, amma shiru har yau babu sakamako ballantana a fitar da caje-cajen da za a gurfanar da shi kotu, idan har ya aikata laifin.

Share.

game da Author