Sakamakon gwajin cutar Korona da aka yi a kasar Amurka Kuma aka fitar ranar Alhamis ya nuna cewa akalla mutum 4,000 sun rasu cikin awa 24 a kasar.
Wannan shine karo na farko da kasar ta samu yawan mutanen da suka rasu a ra a daya a wannan lokaci.
Bisa ga rahotan jaridar ‘Washington Post mutum 3900 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar.
Masana kimiya da masana magungunan sun hada maganin rigakafin korona kuma kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka fara amfani da su sai dai duk da haka mutane sai kara mutuwa suke a dalilin cutar.
Sakamakon jami’ar John Hopkins ya nuna cewa mutum miliyan 21.5 ne suka kamu da cutar a kasar zuwa yanzu. Daga ciki mutum 364,500 sun mutu.
Najeriya
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1565 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –807, FCT-236, Kaduna-79, Oyo-57, Filato-47, Rivers-37, Katsina-35, Edo-30, Sokoto-30, Delta-26, Kebbi-23, Ondo-20, Enugu-18, Abia-17
Ogun-17, Benue-16, Bayelsa-15, Bauchi-14, Niger-13, Kano-10, Borno-6, Imo-5, Ekiti-4, Osun-2 da Jigawa-1
Yanzu mutum 95,934 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 77,982 sun warke, 1,330 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 16,622 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Laraba mutum 1664 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Filato, Rivers, Adamawa da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 34,136, FCT –13,071, Oyo – 4,157, Edo –2,996, Delta –1,944, Rivers 3,738, Kano –2,389, Ogun–2,605, Kaduna –5,717, Katsina -1,671, Ondo –1,863, Borno –823, Gombe –1,359, Bauchi –1,071, Ebonyi –1,120, Filato – 5,381, Enugu –1,445, Abia – 1,082, Imo –789, Jigawa –410, Kwara –1,495, Bayelsa –560, Nasarawa –961, Osun –1,036, Sokoto –455, Niger – 454, Akwa Ibom – 465, Benue – 553, Adamawa – 471, Anambra – 364, Kebbi –215, Zamfara –112, Yobe – 201, Ekiti –426, Taraba- 225, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.