2023: Rashin ‘Yan takara zai tona wa PDP asiri, APC kuma hadama zai gama da ita, Daga Hamisu Bala

0

Na dade ina tunanin yadda PDP za ta fafata da jam’iyya mai mulki a 2023, ganin yadda jam’iyyar sai dada bakin jin ta ke yi a tsakanin hatta magoya bayanta.

Jam’iyyar PDP ya kamata ace ita ce ke caccakar APC a koda yaushe amma sai gashi a cikinta ma arude ‘ya’yan ta suke.

Kusan duka jihohin kasar nan, jam’iyyar PDP na cikin yanayi na Allah ya kyauta musamman a yankin Arewacin Najeriya. Jiha daya tilo da jam’iyyar ke gogan kirji da jam’iyya mai mulki wato APC ita ce jihar Kano ta yadda tafiyar Kwankwasiyya ke matukar ci musu tuwo a kwarya.

Tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso har yanzu ya rike wuta a jihar tare da mabiyan sa ;yan kwankwasiyya. Duk da cew kuwa an zuga bangaren jam’iyyar na neman su dada ruguza tafiyar kwankwaso shi kadai gayya da su da APC a Kano kwamkwasiyya ta ishe su.

Hatta jihohin Inyamirai suna komawa jam’iyyar APC yanzu.

Wata jiha da jam’iyyar ke neman rugujewa karkaf ita ce jihar Kaduna. A jihar Kaduna, kusan za ace babu PDP yanzu. Dan takaran gwamnan jihar a zaben 2019, Isah Ashiru, shine mutum daya tilo da yake tsaye a jam’iyyar a Kaduna. kusan duk sauran musamman ‘yan takaran da suka yi takara da shi duk sun kauce sun koma APC.

Jam’iyyar adawa ta mutu murus a jihar Kaduna. Abin da nake gani kuma mutane ke hasashe shine akwai yiwuwar iata kanta APC ta fashe, ta tarwatse. Hakan zai iya sa wasu kila su koma PDP din su yi takara.

Baban abinda zai kawo matsala kuwa shine, lokacin da za a fara maganan fidda yan takara na jam’iyyu. Nan ne fa ido zai raina fata, zai kai ga kila ya zama ‘iya ruwa fidda kai, wato wanda ya iya katin sa.

Idan da rai da lafiya kamar gobe amma ga mai rai da lafiya za a sha kallo.

Allah ya bamu lafiya, Amin

Share.

game da Author