2023: INEC ta shirya shigo da hanyoyin fasaha kafin gabatowar zabe

0

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta na nan ta na sake nazari kan hanyoyin fasaha da ta ke amfani da su a wajen zabubbuka, da nufin shigo da wadansu sababbi wadanda za su inganta zabubbukan da za a yi daga yanzu zuwa shekara ta 2023.

Daraktan Wayar da kan Masu Zabe da kuma Sashen Yada Labarai na INEC (VEP), Mista Nick Dazang, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taron kara wa juna sani na sashen nasu mai taken “Sake Duban Kundin Wayar da kan Masu Zabe na Kasa” wanda aka yi a garin Keffi, Jihar Nasarawa, a ranar Talata.

Taron, wanda na tsawon kwana biyar ne, INEC tare da hadin gwiwar wata gidauniya mai suna Westminster Foundation for Democracy (WFD) su ka shirya shi.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gefen wajen taron, Dazang ya ce Hukumar Zaben ta soma aikin yin zabe ta hanyar intanet ne tun a cikin 2004 lokacin da ta shigo da tsarin yin rajista da fom-fom waɗanda aka dauka da komfuta.

Ya ce, “Bayan wannan sai a cikin 2010, hukumar ta shigo da tsarin amfani da injinan daukar bayanai kai-tsaye, wanda daga nan kuma ta fadada tsarin amfani da injinan a wajen gudanar da zaben shekarar 2011.

“Saboda haka, mun fara wannan tsarin ne tun a cikin 2004, wanda ya kai mu ga yin amfani da kati mai karanta bayanai a komfuta (Smart Card Reader, SCR) da kuma katittikan zabe na dindindin, wato Permanent Voter Cards (PVCs) wadanda mu ka yi amfani da su a cikin 2015.

“Amma hukumar ta na sake duban fasalin wannan tsarin da nufin daga daraja tare da inganta yadda za a gudanar da zabubbukan 2023.

“Hukumar na so ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha wadanda za su taimaka wajen kambama zabubbuka, sannan su inganta su. Saboda haka dai hukumar na aiki tuƙuru kan wannan.

“Nan ba da jimawa ba, lokacin da hukumar ta gama shawartawa, za ta fito ta bayyana wa ‘yan Nijeriya yadda za a yi wannan din.”

Dazang ya kara da cewa a wajen shigo da sababbin hanyoyin fasahar, INEC za ta sake duban yadda ake amfani da injin karanta katin zabe kuma kila ta shigo da wasu sababbin hanyoyin fasahar wadanda za su yi aiki sumul kalau tare da masu zabe ta hanyar intanet a cikin 2023.

“Hukumar ta na yin aiki a kan hakan a tsawon watanni kuma idan Allah ya yarda nan da watanni kadan hukumar za ta sanar da jama’a matsayin ta.”

Ya ce INEC za ta ci gaba da shigo da sababbin hanyoyin fasaha cikin tsarin gudanar da zabe, ba wai don saboda burgewa ba, sai don hanyoyin fasahar za su amfanar.

Ya yi la’akari da cewa hukumar ba ta yi nadamar amfani da hanyoyin fasahar da ta riga ta shigo da su wajen gudanar da zabubbuka a Nijeriya ba zuwa yanzu, domin sun taimaka gaya wajen inganta tsarin da kuma fayyace gaskiya.

Share.

game da Author