2023: Dawakan Osoba, El-Rufai, Shekarau da Yerima sun fara haniniyar tayar wa APC rikicin jam’iyya

0

Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, Segun Osoba, ya bayyana goyon bayan sa kan cewa lallai a 2023 tilas mulki ya koma Shiyyar Kudancin Najeriya.

Sannan kuma Osoba ya kare ‘yancin da ya ce ya na da shi ya goyi bayan Bola Tinubu don ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a 2023, duk da dai har yau ya ce babu wani wanda ya tuntube daga kudu din da nufin ya mara masa baya.

Bayanin da Osoba, tsohon gwamnan Jihar Ogun ya yi a gidan talbijin na Arise TV, ya zo kwana daya bayan Sanata Ibrahim Shekarau daga jihar Kano ya bayyana cewa babu wani tsarin karba-karba a cikin jam’iyyar APC.

Dama kuma shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fada a cikin Nuwamba cewa a 2023 a nemi nagari wanda ya cancanta, amma batun karba-karba ba zai iya fitar da kasar nan daga mawuyacin halin da ta ke a ciki ba.

El-Rufai cewa ya yi a nemi duk inda nagari ya ke koma a wace shirya, a daina batun karba-karba.

Shi kuwa Osoba, ya ce da shi aka yi zaman ‘maja’ din gambizar jam’iyyun da su ka haifar da APC, Ya kara da cewa duk da Kundin Tsarin Jam’iyya bai tantance cewa akwai karba-karba ba, amma an yi yarjejeniya ta amincewar juna da mutuntakar dattijan taka cewa a 2015 zuwa 2023 za a bar wa dan Arewa mulki. Shi kuma dan Kudu zai yi shugabancin jam’iyya.

Ya ce saboda haka an yarda daga nan kuma mulki zai koma hannun dan Kudu, shi kuma dan Arewa ya rike shugabancin jam’iyya.
Ko Yayin da ra’ayin Osoba ya yi daidai da ra’ayin Rotimi Amaechi, Babatunde Fashola, wasu da yawa a cikin jam’iyyar sun yi fatali da tsarin karba-karba.

Shi ma tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Yerima, ya bayyana muradin sa na fitowa takarar shugabancin kasa a 2023.

Sai dai kuma ya fara sakar tabarmar sa da rudanin cewa babu zancen karba-karba a cikin jam’iyyar APC.

Haka shi ma Shekarau ya nanata a ranar Litinin din nan.

Sai dai Osoba ya ce da shi aka tsara yarjejeniyar dokar kafa APC. Ya ce an yi batun karba-karba a cikin jam’iyyar amma ba a rattaba shi a matsayin doka ba.

Daga nan sai ya ce Tinubu na da ‘yancin tsayawa takara, amma ba kamfen ya ke yi masa ba, kuma bai tuntube shi ya ce ya mara masa baya ba.

Share.

game da Author