2021: Shekarar kawo karshen da matsalolin da suka zame mana kashin kifi a wuya – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta lashi takobin gamawa da matsalolin da suka zame wa kasa kashin kifi a wuya a shekarar bara, wato shekarar 2020.

A jawabin shiga sabuwar shekara da shugaba Buhari yayi ranar Juma’a da Safe, shugaban kasan ya ce wannan shekara ta 2021 ba shekarar wasa ko likimo ba ce, shekara ce wanda gwamnati za ta maida hankali wajen kawo karshen matsalolin da kasa Najeriya ta yi fama da su a 2021.

Sannan kuma ya ce a wannan shekara matasa za su kwankwadi lagwadan gwamnatin sa domin da su za a dama wannan shekara.

Buhari ya ce gwamnati zata zauna da majalisun kasa domin kirkiro dokoki da za su ba matasa dama a rika damawa da su kai tsaye a gwamnati.

Daga nan sai ya jaddada kokarin gwamnatin na ganin an gyara fannin tsaron kasar nan da tabbatar da kawo karshe matsalolin rashin tsaro a kasar nan.

Shekarar 2020 shekara ce da ‘yan Najeriya ba zasu taba mantawa da ita ba, ganin irin matsalolin da aka yi fama da su.

Matsalolin kamar su karayar tattalin arzikin kasa, tsananin talauci, tsadar abinci, rikice rikice, tsananin rashin tsaro, garkuwa da mutane, rashin aikin yi, garkame iyakokin kasa, sannan da uwa-uba annobar Korona.

Shekarar 2020 ta yi wujiwuji da ‘yan Najeriya ta yadda da yawa na jibinta matsalolin da aka yi fama dasu da rashin shugabanci nagari a kasar duk da ko shugaba Buhari ne shugaban kasa.

Share.

game da Author