Ƴan shaye-shaye sun kaɗe – Inji sabon shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa

0

Sabon shugaban Hukumar NDLEA, kuma tsohon gwamnan jihar Legas Buba Marwa ya gargadi masu sha da safarar miyagun kwayoyi a kasar nan da su yi shirin gamuwa da shi muddun ba su dai na wannan sana’a ba.

Marwa ya ce yadda ta’ammali da muggan kwayoyi ya ke bunkasa a Najeriya, Abin tashin Hankali ne matuka. ” Dole gwamnati ta maida hankali wajen kawo karshen yadda musamman matasa ke ragargazar kwayoyi da muggab ababen sha a kasarnan.

Sannan kuma yayi wa ma’aikatan hukumar albishir cewa za a duba duka matsalolin da suke fama da su a baya musamman wadanda suka shafi karin girma, tirenin da dai sauran su.

” Ina son mutane su bude kunnuwar su su saurare ni da kyau. Duk wanda yake mu’amula da masu safarar muggan kwayoyi ko kuma sana’arsa kenan ya sani akwai sabon duba gari yanzu, idan muka kama shi zai yabawa aya zaki.

Sau biyu marwa yana takara shugabancin kasar nan kuma ya yi takarar kujeran gwamnan jihar Adamawa.

Share.

game da Author