Ƴan bindiga na ƙara kwararo mana daga Zamfara da Kaduna –Inji Gwamnan Neja

0

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Bello, ya bayyana a cikin matukar damuwa cewa, dafifin mahara masu garkuwa da mutane da satar dukiyoyi na ci gaba da kwarara zuwa cikin jihar daga Kaduna da Zamfata.

Bello yayi wannan kukan ne a lokacin da ya kammala ganawa a kebe shi da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba.

Ya jaddada wa manema labarai da ke dauko rahoto daga Fadar Shugaban Kasa cewa, Buhari ya yi masa alkawarin za a kakkabe su kakaf.

“Na samu ganawa a tsanake tare da Shugaban Kasa, kuma ya yi alkawarin karin jami’an tsaro da samar da tsaron kan sa a Jihar Neja, nan ba da dadewa ba.”

Da ya ke bayyana wa manema labarai abin damuwa da halin matsalar rashin tsaron da ake ciki, Bello ya ce ya sanar da Shugaba Buhari irin yadda a halin yanzu ’yan bindiga su ka maida hankali wajen yin kaka-gida a Gandun Dajin Bobi Grazing Reserve.

“Babban abin damuwar shi ne yadda mu ka samu masu zuba jari da su ka zuba jari na kudade da kayan aiki a gandun dajin. Amma kuma abin takaici a yanzu sai karin kwararar ’yan bindiga ake samu daga Zamfara da Kaduna.

Ya ce akwai matsala sosai kafin a ce za a iya yin sintirin jami’an tsaro a yankin, domin mota ba ta iya shiga cikin surkukin dajin.

Share.

game da Author