Ƙarin kashi 50/100 na kuɗin wutar lantarki bai shafi waɗanda ke shan wuta na awa 12 a rana ba

0

Hukumar Wutar lantarki ta Ƙasa ta ce ƙarin kuɗin wutan lantarki da ta yi bai haɗa waɗanda ke shan wuta na awa 12 kacal a rana ba.

Idan ba a manta ba ’Yan Najeriya sun tashi da jin labarin karin wutar lantarki har na kashi 50/100, watanni biyu bayan an yi karin kudin ba da dadewa ba.

Karin ya zo kwanaki biyar bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa duk wata hukumar gwamnatin tarayya da ta kasa tara kudade masu yawa a cikin 2021, to shugaban hukumar zai ji a jikin sa.

Haka abin ya faru a farkon shekarar 2020, inda aka yi karin kudin wutar lantarki.

Bayan an sake yin wani karin a cikin watan Agusta, sai kuma a cikin Satumba bayan da gwamnati ta ga ana ta sukar karin kudin wuta da na fetur, sai ta bayyana cewa “an yi karin domin ’yan Najeriya su ji dadi.”

Yanzu kuma an sake yin kari har na kashi 50/100, kamar yadda Hukumar Kula da Makamashi ta Kasa (NERC) ta bayyana.

Wannan kari dai NERC ta yi shi ga dukkan kamfanonin sayar da wutar lantarki su 11 na kasar nan. Kenan su kuma za su lafta karin kudin kan kwastomomin su, mai halin biya da kuma talaka.

Shugaban Hukumar Gudanarwar NERC, Sanusi Garba ne ya saw a takardar sanarwar yin karin hannu, wadda aka fitar a ranar 30 Ga Disamba, 2020.

Wannan ya na nufin karin kudin ya fara aiki tuni, tun a ranar 1 Ga Janairu, 2021.

Sanarwar ta ce an yi karin kudin bayan yin la’akari da cewa tsadar rayuwa a kasar nan ta kai kashi 14.9%, sannan kuma zuwa Disamba karshen wata naira 379.4 ake canjar dala.

Dama kuma ko a farkon 2020, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Gwamnati ta bude sabuwar shekarar, waccan ta 2020 da karin kudin wutar lantarki

Aikin farko da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a ranar 1 Ga Janairu, 2020, shi ne karin kudin wutar lantarki har zuwa kashi 78% bisa 100% daga yadda ake shan wutar tun daga 2015.

Luguden Karin Kudin Lartarki Cikin 2020:

Daga 1 Ga Janairu, 2020 za a fara shan wutar lantarki a sabon farashin da ba na 2015 ba, kamar yadda Hukumar Kayyade Farashi da Adadin Wutar Lantarki ta Kasa, NERC ta fitar da sanarwa.

NERC ta fitar da wannan sanarwa ce ga dukkan Kamfanonin Saida Wutar Lantarki 11, wato Discos a ranar 31 Disamba, 2019. Amma dai sai ranar Asabar ce NERC din wallafa labarin karin farashin a shafin ta.

Shugaban Hukumar NERC, Joseph Momoh da Shugaban Kula da Lasisin Kamfanonin Saida Lantarki, mai suna Defe Akpanye ne suka sa wa sanarwar hannu, wadda tuni aka raba wa Discos 11 ita.

Wannan sanarwa na dauke da bayani dalla-dalla na karin kudin da kowane mai shan wutar lantarki zai rika biya daga ranar 1 Ga Janairu, 2020 kenan.

Misali, an yi karin kashi 57% bisa 100% na farashin lantarki a Ikeja, Lagos, yayin da a Enugu kuma aka yi karin kashi 77.6.

Mazauna Enugu na biyan naira 13.4 ga kowane ‘yunit’ na wuta kwh tun daga 2015. Amma daga 1 Ga Janairu, 2020 za a rika cajin su naira 21.8 kowane ‘yunit’.

Dalilan Karin Kudin Lantarki A 2020:

Kadan daga dalilan karin kudin lantarki da Hukumar NERC ta bayar na karin kudin wuta, sun hada da karin farashin kayayyaki da ya haifar da kudade masu yawa ke sayen kaya kalilan, zuwa karin kashi 11.3 daga Janairu 2019 zuwa Oktoba 2019.

Sai kuwa yadda farashin dala daya da gwamnati ta kayyade a kan naira 306, amma sai jidalin naira 3 hau kan ta, zuwa 309, sai kuma yadda farashin man gas ya kai dala 2.50 a kowace ‘metric tons’ milyan daya.

A karshe Hukumar NERC ta gargadi Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Kasa, TCN cewa shi za a kama da laifi idan wani kamfanin Saida Lantarki ya ki bin wannan umarni na karin kudin wutar lantarki.

Share.

game da Author