ZAZZABIN CIZON SAURO: Yaduwar cutar ya ragu zuwa miliyan 9 cikin shekaru 20 da suka wuce

0

Rahoton da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar ya nuna cewa an samu ragowan yaduwar zazzabin cizon sauro zuwa miliyan 9 a cikin shekaru 20 a kasashe 87 da suka fi fama da cutar.

Rahoton ya kuma nuna cewa yaduwar cutar ta ragu daga miliyan 238 a shekarar 2000 zuwa miliyan 229 a duniya.

WHO ta fitar da wannan rahoto ne ranar Litini din wannan mako.

Bayan haka an samu ragowan yawan mutanen dake cikin hatsarin kamuwa da cutar a duniya daga 1000 zuwa 80 a shekaran 2000, zuwa 58 a 2015 sannan zuwa 57 a shekaran 2019.

“Tsakanin shekaran 2000 da 2015 bullowar cutar ya ragu zuwa kashi 27 sannan tsakanin shekaran 2015 da 2019 ya sake raguwa da kashi biyu.

Bayan haka adadin yawan mutanen da cutar ta kashe ya ragu daga 100,000 zuwa 25 a shekaran 2000 sannan ya sake raguwa zuwa 12 a shekaran 2015 sannan zuwa 10 a 2019 a duniya.

Zuwa yanzu mutum miliyan 215 ne suka kamu da cutar a Nahiyar Afrika a shekaran 2019.

A dalilin haka ya sa Nahiyar Afrika ta ci gaba da zama fannin da ta fi fama da yaduwar cutar a duniya.

kashi 27 ne suka kamu da cutar sannan kashi 23 sun mutu a dalilin cutar a shekaran 2019 a Najeriya.

An kuma samu ragowan kashi 17 a yawan yara ‘yan ƙasa da shekara biyar da cutar ke kashewa daga kashi 84 a shekaran 2000 zuwa kashi 67 a 2019.

An samu raguwar yaduwar cutar a kasashen Afrika daga 680,000 a 2000 zuwa 384,000 a 2019.

Rahoton ya kuma nuna cewa matakan dakile yaduwar cutar da aka dauka ya taimaka wajen kare mutum miliyan 1.5 daga kamuwa da cutar da kuma rasa rayuka da yawa.

Zazzabin cizon sauro

Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro Wanda idan ba a gaggauta Neman magani ba cutar ka iya yin ajalin mutum.

Cutar ta yi ajalin mutane da yawa a duniya duk da maganin warkar da cutar da ake da shi.

Zuwa yanzu Nahiyar Afrika ce bangaren duniyan da wannan cutar ta yi wa katutu.
Sannan a kasashen Afrika Najeriya ce kasan da ta fi fama da cutar.

A shekaran 2019 WHO ta ce kimanin dala biliyan uku be za a bukata wajen yaki da cutar amma kasashen da suka fi fama da cutar sun tara dala miliyan 900 kudin yaki da cutar.

Share.

game da Author