A shirin yin zaben cike gurbi a mazabar Bakura da Talatan Mafara wanda za ayi ranar Asabar, magoya bayan manyan jam’yyun Najeriya biyu, APC da PDP sun goge raini a garin Bakura.
Akalla mutum biyu ne aka kashe sannan wasu da dama sun arce da muggan raunuka a jikin su a dalilin harbin bindigogi da hasalallun matasan suka rika yi wajen kare jam’iyyar su.
Sai dai bayan haka gwamnan jihar ya saka dokar hana walwala a kananan hukumomin Bakura da Talatan Mafara.
Tun kafin taron kamfen din da ya ta da jijiyoyin wuyan magoya bayan jam’iyyun, Gwaman jihar Bello Matawalle ya yi gargadi da korafin cewa Ƴan APC na cakalar ƴan PDP.
Sannan yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sa a binciki musabbabin tada zaune tsaye da ya faru a Bakura sannan kuma da hukunta wadanda aka samu da laifi.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsaida da ranar Asabar don zaben cike gurbi na kujerar Majalisar Dokoki ta jihar, inda jam’iyyu 14 ke fafatawa.
Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa magoya bayan jam’iyyar PDP mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta APC sun yi artabu wajen ko wanne cikinsu zai yi kamfen a filin taron dake hedikwatar karamar hukumar da ke garin Bakura.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usman Nagogo, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa 14 da ke halartar zaben maye gurbin da su ja wa magoya bayansu kunne sannan su lallashe tunda wuri domin a cewar sa rundunar ba za ta yi kasakasa ba wajen hukunta duk wanda ya nemi ta da zaune tsaye a lokacin zaben cike gurbin da za ayi ranar Asabar.
Discussion about this post