Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta yi alƙawarin cewa dukkan jihohi 36 da ƙasar nan da kuma yankin Abuja za su amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na Agajin Kyautar Kuɗi ga Matan Karkara, wato ‘Special Cash Grant for Rural Women’.
Ta bada wannan tabbacin ne a wajen taron ƙaddamar da shirin a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ranar Alhamis, 3 ga Disamba, 2020.
A jawabin da ta gabatar a taron, ministar ta ce al’ummar Jihar Imo su ma masu cin moriyar shirin nan ne na tura wa mata agajin tsabar kuɗi, wato ‘Conditional Cash Transfer’ wanda aka ɗauki gidajen marasa galihu guda 11,697, da shirin N-Power, da shirin ciyar da ɗalibai da ke zaune a gida (Home Grown School Feeding) da kuma shirin tallafin yin sana’a na GEEP, wato ‘Government Entrepreneurship Empowerment Programme’.
Sadiya ta ce, “Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi maida hankali ga matsalolin marasa galihu a ƙasar nan tun daga 2015 kima mutum 150,000 ake sa ran za su ci moriyar shirin ta na bai wa matan karkara tallafin kuɗi a dukkan ƙananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan.
“Tun daga farkon shirin nan na ‘National Social Investment Programme’ a matsayin wani tsari na yaƙar talauci a tsakanin yawanci al’ummar mu, rayuwar talakawa faƙirai a Nijeriya ta inganta sosai. Da yawa daga cikin irin waɗannan mutanen sun samu cikakken sauyin rayuwar su.
Saboda haka, ina farin cikin ganin taruwar ku a nan domin ƙaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya na raba wa matan karkara agajin kuɗi, wanda ya na daga cikin shirye-shirye masu yawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu ta fito da su saboda ta ɗaga rayuwar yawancin jama’a daga ƙuncin rayuwa.
Ministar ta ƙara da cewa manufar wannan agajin musamman ɗin ita ce a kai tsabar kuɗi kai-tsaye ga gidajen da su ke buƙata wanda hakan zai taimaka wa iyalan wajen sayen kayan masarufi, yin amfani da kayan magance matsalar yunwa sayen kayan abinci da kula da lagiyar jiki, da shigar da yara da biya masu kuɗin makaranta da dai sauran su.
Ta yi kira a gare su da su yi amfani da kuɗin wajen yin ƙananan kasuwanci wanda hakan zai taimaka wa dogaro da kai da samun sana’a.
Tun da farko, sai da mai ba Gwamnan Imo Shawara kan shirye-shiryen cigaban al’umma na SDGs da ayyukan jinƙai, Gimbiya Christina Udeh, ta ce ziyarar da ministar ta kai a jihar, shaida ce da ke nuna yadda ta ke damuwa da matsalolin tattalin arzikin al’ummar Jihar Imo, ciki har da naƙasassu da faƙirai da ke zaune a yankunan karkara.
Ta ce, “Shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin kuɗi ga matan karkara zai rage fatara da yunwa, ya hana marasa galihu cigaba da faɗuwa cikin ramin fatara da yunwa kuma ya ba su kariya daga bala’o’i.
“Haka kuma ministar ta zo nan ne domin ta ƙaddamar da Ranar Mutane Masu Fama da Nakasa ta Duniya sannan ta raba N20,000 ga kowace macen karkara domin ta ja jari wanda zai taimaka ya sauya mata rayuwar ta da halayya.”
Daga bisani ministar ta miƙa tsabar kuɗi ga wasu daga cikin matan karkarar.
Matan sun bayyana godiyar su ga Shugaba Buhari saboda wannan tsari da ya fito da shi.