Za mu kara samar da aikin yi a fannonin aikin gona, nishadantarwa da albarkatun kasa – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada kokarin gwamnatin sa wajen ganin ta kara samar da madafun aikin yi ga matasa, ta hanyar karfafa hanyoyin sana”o’in masu zaman kan su da su ka hada da harkokin noma, albarkatun kasa, nishadantarwa da fasahar zamani.

Buhari ya yi wannan bayani a Taron Manyan Jami’ai na 42, na Cibiyar Nazarin Gudanar da Mulki da Tsare-tsare da ke Kuru, Jos.

An gudanar da taron na wannan shekarar ce a Babban Zauren Taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Villa, Abuja.

Abin da aka sa gaba a wannan karo shi ne, “Kalubale da Dama Kan Yadda Al’umma Ke Kara Yawa Bisa Ma’aunin Ci gaba Dan Adam.”

Buhari ya ce wannan Maudie’in taro ya zo daidai da halin da ake ciki.

“Hakan ya zo daidai da halin da kasar nan me ciki. Don haka ina tabbatar maku cewa idan ku ka gama tattaunawa, duk abin da ku ka kawo na shawarwari, za mu yi aiki da su domin kara dora kasar nan bisa turbar ci gaban bunkasa al’umma da kasa baki daya.

“Wannan gwamnati ta rike turbar inganta rayuwa da gina al’umma, musamman matasa da marasa galihu.”

Shugaba Buhari ya shaida wa masu halartar taron yadda gwamnatin sa ta kan fadada inganta tattalin arzikin kasa ta fannoni daban-daban, maimakon dogara kacokan kan man fetur.

Share.

game da Author