Ministan Tsaro Bashir Magashi ya sha alwashin cewa za a ceto daliban Sakandaren Kwana ta Kankara da ke Jihar Katsina a cikin ruwan sanyi.
Ya yi wannan alkawarin ranar Lahadi a Katsina, lokacin da ya je wa Gwamna Aminu Masari jaje.
Ya ce ya yi amanna za a ceto yaran ba tare da an yi asarar ran yaro ko daya ba.
Sannan kuma ya ce hukumomin tsaro na leken asiri da bibiyar halin da ake ciki da yaran.
“Na samu bayanai daga Kwamishinan ‘Yan Sanda da Brigade Kwamanda. Za a tabbatar an ceto su da hanzari kuma ba tare da wani ya rasa ran sa ba.
“An gano inda su ke da duk wani motsi da aka yi ko ake yi da su. Saboda haka ina tabbatar da cewa za a kwato cikin ruwan sanyi.”
Magashi ya ce a kwantar da hankali, kuma a yi addu’ar dawo da su ba tare da asarar ran ko dalibi daya ba.
Bayanin Magashi ya zo bayan da Gwamna Masari ya bayyana cewa yaro 333 ne ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.
Cikin 2019 sai da masu garkuwa su ka tasa mutum 76 zuwa cikin daji, a garin Wurma, cikin Jihar Katsina.
Wannan shi ne karo na uku ana satar dalibai bayan na Chibok a Jihar Barno da Dapchi a Jihar Yobe.