Za a yi kidayar ’yan Najeriya cikin yuni, 2021 –Shugaban Hukumar Kidaya

0

Shugaban Hukumar Kidaya na Kasa Nasir Issa Kwarra, ya bayyana cewa hukumar kidaya, NPC ta shirya gudanar da aikin kidayar ’yan Najeriya cikin watan Yunin 2021.

Ya ce aikin kidayar zai fara daga tsakaiyar 2021 kenan har zuwa farkon 2022.

Kwarra yay i wannan jawabi a taron manema labarai, inda ya bada bayanin irin ci gaban da NPC ta samu a karkashin sa, dangane da shirye-shiryen fara aikin gudanar da kidayar.

“Mu dai a na mu bangaren, mun rigaya mun kimtsa. Za mu iya fara aikin kidayar jama’a daga watan Yuni, 2021 zuwa farkon 2022.

Ya yi karin bayanin cewa ya na sane da yadda aka samu tsaikon fara aikin kidayar har tsaron shekaru biyar. Sai dai kuma ya ce duk wannan lokacin NPC na tuntubar gwamnatin tarayya domin a bada umarni.

Rabon da a yi kidayar jama’a a Najeriya tun cikin 2006.

“Shirye-shiryen fara kidayar jama’a ya kankama ka’in-da-na’in. mun san an samu jinkirin tsawon shekaru biyar, amma dai mu a na mu bangaren mu na tuntubar gwamnati domin a ba mu umarni faraway kawai.” Inji Kwarra.

Ya ce tuni NPC ta fara aikin tantancewa da rarrabe kan iyakokin tsarin kidaya na yankuna da garuruwa da jihohi.

“Tuni harm un kammala tantance kananan hukumomi 460 na fadin kasar nan. A yanzu kuma mu na kan tantance kananan hukumomi 96. Saboda haka mu na sa ran zuwa watan Yuni za mu iya kammala tantance dukkan kananan hukumi 774 na fadin kasar nan kakaf. Kun ga daga nan sai fara kidayar jama’a kawai.”

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labari a cikin Oktoba, inda Shugaba Muhammdu Buhari ya amince a kashe naira bilyan 10 wajen aikin shata kan-iyakoki a Kananan Hukumomi 546 a kasar nan.

Aikin wanda aka fi sani da Enumeration Area Demarcation (EAD), ya na cikin shirin kidayar adadin al’ummar Najeriya arankatakaf da za a yi ba da dadewa ba.

Gwamnatin ta tsara aikin shata tantance iyakokin ne domin a ji saukin gudanar da kidayar.

A bangaren kidayar, Buhari ya kuma amince da kara naira bilyan 4.5 cikin kasafin 2021, domin a kammala aikin tantancewar, wanda shi ne sharar-hanyar aikin kidayar da za a fara gadan-gadan.

Shugaban Riko na Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Eyitayo Oyerunji ne ya bayyana haka, tun kafin Buhari ya nada Issa Kwarra shugabancin NPC.

“Cikakkun bayanan abin da aikin EAD ke samarwa, abu ne mai marukar muhimmanci ga aikin sa-ido da jami’an tsaro ke gudanarwa da kuma afkuwar manya da kananan laifuka a yankuna daban-daban.” Inji Oyetunji.

“Shugaban Kasa ya kara wa wannan shiri karfi ta hanyar kara naira bilyan 45 cikin Kasafin 2021 domin kammala shirin, wanda sharar-hanya ce ga aikin kidayar da za a gudanar.” Inji shi.

Da aka tambaye shi ko yaushe ne za a fara aikin kidayar, sai ya ce har yau ba a sa ranar farawa ba.

Amma dai ya ce hakan alamu ne tabbas da ke nuna cewa nan ba da dadewa ba za a fara aikin kidayar.

Rabon da a kidaya ‘yan Najeriya tun cikin 2006.

Oyetunji ya ce an rigaya an kammala aikin shata tantance kananan hukumomi 228 a fadin jihohin Najeriya 36 da Gundumar FCT Abuja.

Ya ce za a ci gaba da aikin shata iyakokin kashi na 10 daga ranar 5 zuwa 29 Ga Oktoba. Kuma akwai aikin bada horo ga ma’aikatan da za a dauka da kuma fita ana aiki wurjanjan.

Share.

game da Author