Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kwankwadi ruwan ragargaza daga ‘yan Najeriya kan cewa da yayi wai majalisa bata da ikon yi wa sammacin ya bayyana a gabanta ba.
Malami ya ce majalisar Kasa bata da ikon yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sammaci ya bayyana a gabanta.
Wannan kalami na Malami ya harzuka ‘yan Najeriya inda suka yi tururuwa zuwa shafin tiwita suna ragargazar sa.
Idan ba a manta ba, majalisar Tarayya ta gayyaci Buhari ya bayyana a gabanta domin yi musu bayani kan yadda matsalar tsaro yaki ci yaki cinyewa a kasa Najeriya.
Bayan mika wannan gayyata ga shugaba Buhari, ya amsa gayyatar inda ya ce zai bayyana a gaban su.
Hakan bai yiwu ba, bayan gwamnonin jam’iyyar sun ce ba za su yarda Buhari ya bayyana a majalisa ba, suna mai cewa akwai wata makarkashiya da ‘yan jam’iyyar adawa suka shirya wa.
Gwamnoni sun ce sun bankado wani shiri da mambobin jam’iyyun adawa dake majalisar na sun kunyata shugaba Buhari idan ya bayyana a gaban su.
” Mun gano cewa mambobin jam’iyyar adawa sun shirya wani makircin su kunyata Buhari a majalisar idan ya bayyana. Idan muka bari hakan ya faru zai zama cin fuska ga jam’iyyar mu mai daraja, jam’iyyar APC da kuma shi kansa shugaban kasa.
Wani dan majalisa da ya halarci taron gwamnonin da jiga-jigan yan majalisar ya ce babu gaskiya cewa wai za a kunyata Buhari a majalisar.
” Mu ne muka fi yawa a majalisar, babu yadda za a ce wai muna gani za a kunyata shugaban mu. Amma kuma bayyanar sa gaban majalisa zai ba mutane daman sanin abinda Buharin yake yi kai tsaye. Sannan muma za mu samu sauki a shiyoyin mu.