‘Yan Najeriya su daina danganta bala’o’in Najeriya cewa daga Allah ne – Obasanjo

0

“Ai idan muka aikata hairan, to tattallin arziki zai bunkasar da ya kamata ta yi.” Inji Obasanjo.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya gargadi shugabannin kasar nan su daina tabka shirme, sannan daga baya su koma su na cewa duk wani bala’in da ya afka wa kasar nan wai mukaddari ne da ga Allah.

Obasanjo ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa sakon sa da ya yi a Dakin Karatun sa da ke cikin gonar sa ta Otta, da ke Abeakuta, babban birnin Jihar Ogun.

“Idan mu na da shugabannin da su ka san abin da su ke yi, to babu wani dan Najeriya ko daya tal da zai kwanta barci cikin sa da yunwa saboda bai ci ba, bai kuma sha ba.

“Idan mu ka aikata hairan, to tattalin arziki zai bunkasa kamar yadda ya kamata ya bunkasa din. Ina jin dadin wani kirari da akan yi wa wata makaranta, ‘ka yi addu’a kuma ka yi aiki tukuru’. Don haka ni ban san wand azan fata kawowa da farko ba. Amma dai tilas a hada addu’a da tashi a yi aiki tukuru. Haka aiki tukurun shi ma sai an hada da addu’a.”

Da ya ke magana kan shekarar 2020, ya ce, “mun shiga cikin matsalar tsaro, kuma mun fada matsin tattain arzikin kasa da kuncin rayuwa. Ga kuma cutar korona.

“Wasu masu karar kwana ta ritsa da su sanadiyyar rashin tsaro. Wasu cutar korona ce ta kashe su. Wasu kuma kuncin rayuwa ce ajallin su. Sai dai mu yi masu fatan samun rahamar ubangiji.”

Daga nan ya ce ‘yan tilas ‘yan Najeriya su zage damtse su yi aiki tukuru cikin 2021.

“Mun yi amanna cewa sai mun tashi tsaye tukuru a kasar nan, tare da hadawa da addu’a din a cikin 2021 domin shekarar ta kasance mana mai albarka da yalwa. Amma fa wannan albarkar da yalwar arzikin ba za su tabbata ba sai an yi aiki tukuru.

“Mu daina dora wa kan mu abu muna cewa Allah ne ya dora mana. Bai kamata a ce Najeriya matalauciyar kasa ba ce. Bai kamata a ce akwai dan Najeriya ko da guda daya mai kwanciya ba tare da ya ci abinci ba. Idan ya kasance ana irin wannan rayuwar, to fa hakan zabin shugabannin mu ne da kuma zabin mabiyan su.”

Share.

game da Author