Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da Korona, Boss Mustapha, ya bayyana wa manema labarai yadda mutum tara gaba dayan ‘yan gidan sa, su ka kamu da cutar korona, ciki har da yaro dan shekara daya tal.
Mustapha, wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya kara da cewa a cikin mutum tara da su ka kamu a gidan sa, hudu duk ‘ya’yan sa ne.
Ya ce yayin da aka gwada shi da matar sa ba su dauke da cutar, har yanzu sauran su na can sun a samun kulawa, irin wadda likitoci da jami’an lafiya ke bai wa wadanda su ka kamu da cutar korona.
” Wato abin fa bala’i ne muraran. Ni dai ban kamu ba, amma maganar gaskiya kam a ce ’ya’yan ka hudu a cikin gidan ka su kamu da korona, ba karamin bala’i ba ne.” inji Mustapha.
“Idan ka na matsayin uba, ga yaran ka sun kamu da korona, abin tashin hankali ne gagarimi. Saboda haka kowane uba ya tabbatar da ya yi bakin iyar kokarin da zai kara kan sa da iyalan sa daga kamuwa da cutar korona.
Tuni dai aka bada sanarwar sake barkewar cutar korona karo na biyu, kuma aka shawarci jama’a da gargadin cewa kowa ya dauki matakin kare kan sa.
An kuma umarci jihohi su kulle gidajen giya, gidajen holewa da wuraren taron gangamin ‘yan shan shagalin nishadin hululu.
Haka nan an hana taron jama’a da ya haura mutum 50.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda korona ta bulla gidan Sakataren Gwamnati Boss Mustapha, shi da matar sa sun killace kan su
Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha a matar sa sun killace kan su, bayan an samu wasu daga cikin iyalan sa sun kamu da cutar korona.
Boss Mustapha ne da kan sa ya yi wannan sanarwa, inda ya ce bayan an samu wasu a gidan sa dauke da cutar, an yi masa gwaji shi da matar sa, amma dai ba a same su da cutar ba.
Ni Da Mata Ta Mun Killace Kan Mu:
“Ina sanarwa cewa ni da mata ta duk mun killace kan mu kamar yadda ka’ida ta gindaya. Kuma zan rika gudanar da ayyukan ofis daga gida.
“Wadanda aka samu da cutar babu wata alama mai nuna su na dauke da cutar korona a jikin su. Mu din ma da aka yi wa gwaji, ba a same mu dauke da cutar ba.” Inji Mustapha, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yaki Da Korona na Najeriya.
Korona da bulla gidan Sakataren Gwamnatin na Najeriya, kwanaki uku bayan ya zargi masallatai da coci-coci da laifin sakacin sake fantsamar korona a kasar nan.
A ranar Lahadi sama da mutum 400 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.
Sannan kuma waau yawan mutuwar da ake yi a kasar nan ana dangantawa ne da cutar korona.
Tuni dai aka umarci jama’a kowa ya kara yin kaffa-kaffa daga kamuwa da cutar.