‘Yan bindiga sun kashe ‘ yan sanda 3 dogarai 5 a wani harin kwantar bauna da suka kaiwa tawagar sarkin Kauran Namoda a Titin Zariya – Funtua.
Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun afkawa jerin gwanon motocin sarkin ne ba tare da sun sani ba inda nan take suka kashe’ yan sanda uku nan take, sannan suka kashe dogaran sarkin su biyar.
Rahotannin sun nuna cewa sarkin Sanusi Muhammad-Asha da matarsa basu samu ko kurzuna ba a jikin su.
Sun kwana a wani wuri a Funtuwa bayan tsira da suka yi daga harin.
Za a yi jana’izan wadanda suka rasu bayan sallar Juma’a a Zamfara.