Farfajiyar Kannywood ta fada cikin mawuyacin yanayi, saboda harkallar masu satar fasaha wato ‘Copyright’. Wannan abu ya gurguntar da hanyoyin cinikayya, da siye da siyarwar fina-finai a farfajiyar.
Mutane da dama basu iya kallon fina-fina kamar yadda aka saba a baya saboda faduwa da masu shirya fina-finai ke yi a duk lokacin da suka saki sabon fim a kasuwa.
Kafin su saida 10 masu satar fasaha sun saida 100. Abin dai sai ya zamo kawai kamar ana yi wa wasu aiki ne. Sai ka kashe kudin ka sai wasu can su amfana da aikin kai kuma ko-oho.
Hakan ya sa dole masu shirya fina-finai suka koma haska fina-fina su a Sinima.
Sai dai kuma karancin Sinima a musamman yankin Arewa ya kawo wa masu shirya fina-finan Kannywood cikas sannan kuma da tsadar shiga kallo.
PREMIUM TIMES ta tattauna da fitaccen jarumi, Nuhu Abdullahi kan ko ina aka dosa.
” Abu na farko da zan ce a nan shine in yi muku albishir cewa mun samu wani hamshakin mai kudi kuma dan asalin kudancin Najeriya, wanda yaba Kannywood kudunmawar naira miliyan 600 domin su fadada farfajiyar. Wannan gudun mawa da Jack-rich ya bamu ya yi matukar faranta mama rai domin zai taimaka mana wajen fadada sana’ar mu a wannan lokaci da muka fada cikin kangi na kokawa da masu satar fasaha.
” Gwamnan Jihar Kaduna ma ya tallafa wa Kannywood da wawukeken fili a jihar da kuma yi mana alkawarin tallafa mana da naira miliyan 100 a lokacin da za mu fara aiki a filin. Wannan abin yaba wa ne da cigaba. Sannan kuma da jinjina da muke yi wa Musa Dijima, wanda shima yana cikin wadan da ke tallafawa farfajiyar a kai akai.
Akarshe jarumi Nuhu Abdullahi ya roki sauran attarai musamman ‘yan Arewa da su tallafa wa farfajiyar domin ta iya ci gaba da tsayawa da kafafuwanta.
Ya roki gwamnoni su tallafa musu da filayen da za su gida dakunan kallon fina-finan su kamar yadda yake a kasashen da suka ci gaba.