Yadda na kashe dan achaba, na saida da babur din sa na siya irin doya – Lawal

0

Wani manomi da rundunar ƴan sandan jihar Ekiti ta damke mai suna Ayo Lawal ya kashe ɗan achaba kuma ya siyar da babur dinsa domin siyo irin doya.

Lawal mazaunin Odo Oro ne a karamar hukumar Ikole inda ya yi bayanin cewa ya aikata haka ne bisa ga hudubar wani abokinsa mai suna, Sule Abdullahi.

” Abokina Abdullahi ne ya bani shawara in kashe Isaac kuma wai mu birne shi a gona ta.

“Abdullahi ya ce idan muka kashe Isaac sai mu saida da babur. Naws kason kudin babur din zai siya mun irin doya.

Kakakin rundunar ƴan sanda Sunday Abutu ya tabbatar da haka yana mai cewa rundunar ta kama Lawal, Jimoh Ojo sannan sun fantsama farautar Abdullahi da sauran wadanda suka aikata wannan mummunar abu.

Bayan haka rundunar ta damke wani Yakubu Aliyu shahararren mai garkuwa da mutane a dajin Ilemesho Ekiti dake karamar hujumar Oye.

Aliyu ya shaida wa jami’an tsaron cewa yana cikin kungiyar maharan da suka yi garkuwa da tsohon kwamishinan aiyukkan noma Folorunso Olabode da ya yi aiki da gwamna Kayode Fayemi.

Ya ce abokan aikinsa sun hada da Dani, Gide, Danja, Bello, Sidi, Babi, Ali da Wada.

Rundunar ta kama Wada da Ali sannan har an yanke musu hukunci a kotu.

Abutu ya ce an gyara ofishin ƴan sandan dake Ikere Ekiti bayan masu zanga-zangan EndSARS sun rusa shi.

Ya kuma ce an aika da akalla ƴan sanda ofishin domin tsaro a yankin.

Share.

game da Author