Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ‘yan uwana masu daraja, kamar yadda kuka sani ne wasu ‘yan ta’adda sun kai hari shekaran jiya, ranar juma’ah, 11/12/2020 da daddare, a inda suka sace yara ɗalibai a makarantar sakandaren Ƙanƙara, da ke jihar Katsina, a nan kasar mu Najeriya.
Ya ku al’ummah, ku sani, wannan abun takaici ne, abun bakin ciki, abun tausayi, abun tayar da hankali, kuma abun mamaki, ace an sace yara, dalibai, manyan gobe, a wannan makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara da ke jihar Katsina. Wannan wani abu ne dake nuna yadda matsalar tsaro take kara yin kamari a Kasar nan, wanda dole ne duk wani mai imani yayi Allah-waddai da shi, kuma a fito ayi magana da babbar murya, domin hukumomin da abun ya shafa, su kawo karshen wannan bala’i!
Ta yaya za’a ce, a Najeriya yanzu mutane basu da ikon tura ‘ya ‘yansu makaranta? Kawai sai wasu ‘yan iska su kai hari, su dauke su? Kasa ta zama sai kace kasar da babu shugabanni? A haka zamu ci gaba da rayuwa cikin tashin hankali da damuwa na rashin tsaro?
Ina mai jajantawa iyayen wadannan yara da aka sace, da Gwamnati da kuma dukkanin al’ummar jihar Katsina, da dukkanin ‘yan Najeriya akan wannan ibtila’i. Ina addu’a da rokon Allah Ta’ala Ya dawo muna da wadannan yara lafiya cikin aminci da koshin lafiya, kuma ina rokon Allah, yayi muna maganin wadannan matsaloli da ke addabar kasar mu, amin.

Sannan muna kira ga shugabannin wannan kasa, da hukumomin tsaron wannan kasa da duk wani mai ruwa da tsaki a wannan sha’ani na tsaro, da su ji tsoron Allah, su dauki matakan da suka dace, cikin gaggawa domin su ceto wadannan yara, wadannan dalibai, bayin Allah da aka sace.
Ba yau ne aka fara satar ‘ya ‘yan mutane ba a makarantun Najeriya, ya sha faruwa a makarantu da dama. Misali, ya faru a makarantar Chibok, jihar Borno. Ya faru a makarantar Dapchi, jihar Borno. Kuma ya faru a makarantar Buni Yadi da ke jihar Yobe, da ma dai wurare daban-daban. Yanzu domin Allah haka zamu ci gaba da rayuwa a wannan kasa? Tsaro ya zama wahala. Duk lokacin da ‘yan ta’adda suka ga dama sai su tafi makarantu su sace ‘ya ‘yan mutane, babu-gaira-babu-dalili? Ko kuma su sace duk wanda suke so su sace, sai an biya kudi kafin su sake shi?
Yanzu domin Allah, mun san irin halin da iyayen wadannan yara suke ciki, na damuwa da bakin cikin sace yaran su, abun kaunarsu, sanyin idonsu, kuma abun alfaharinsu? Yanzu domin Allah, da kai ne aka sace ‘ya ‘yanka, yaya zaka ji? Mu sani, yara fa ba abun wasa bane. Biyo ni, ya kai dan uwa, domin ka ji irin yadda addinin Musulunci ya dauki yara, kuma ya karrama su!
Ya ku bayin Allah, kasancewar yara a Musulunci sune dadin rayuwar duniya, sune adonta da kuma kawarta, sannan kuma sune masu sanyaya ran iyaye da al’ummah, shi yasa Annabi Muhammad (SAW) ya basu kyakkyawar kulawa, a inda ya wajabta hakkoki masu tarin yawa saboda su. Babbar kulawar da addini ya ba yara ita ce wadda ya basu tun kafin haihuwarsu, shi yasa Annabi Muhammad (SAW) ya umarci iyaye (maza) yayin neman aure, da su zaba wa ‘ya’yansu iyaye (mata) nagari, a inda yace:
“Ana auren mace ne saboda abubuwa guda hudu: domin dukiyarta, ko matsayinta, ko kyawonta, ko addininta, amma ka ribatu da ma’abuciya addini sai kaci nasara.” [Bukhari]
Hakanan kuma Annabi (SAW) ya umurci mata, su ma yayin aure da suyi irin wannan zabin, a inda yace:
“Idan wanda kuka yarda da addininshi da halinshi yazo neman aure, to ku aura masa, idan ba kuyi hakan ba kuwa, hakika za ku haddasar da fitina da barna mai girma a doron kasa.” [Tirmizi]
Saboda haka ne ma addinin Musulunci ya sanya zaben mace ta gari a cikin jerin hakkokin da yaro yake da su akan mahaifinsa.
Hakika babu shakka, cewa wannan zabi da addini ya bai wa dukkanin bangarori guda biyu na mace da kuma na namiji, zabi ne mai matukar amfani ga rayuwar yaro, sakamakon aure tsakanin mutanen kirki, domin yaro ya taso a gida mai tarbiyyar addini, gidan girma, kuma gidan mutunci.
Kulawar da addini ya bai wa yara bata tsaya a nan kawai ba, harta kai ga mahaifiyarsu, yayin da take dauke da cikinsu, sai Annabi Muhammad (SAW) ya bata damar shan azumi, domin tausayawa dan nata.
Hakanan kuma yayi umarni da kiran Sallah a kunnen yaro lakacin haihuwarsa, saboda ya zamanto farkon abun da za ya fara shiga kunnenshi shine, shaida girman Allah da kuma kadaitashi.
Hakanan kuma Annabi Muhammad (SAW) ya umurci iyaye da su zaba wa ‘ya’yansu sunaye masu kyawo, wadanda suke kunshe da ma’anoni da kuma siffofi kyawawa wadanda zasu rinka sa su nishadi da kuma alfahari da jin dadi, ba wadanda suke dauke da siffofi na kaskanci da wulakanci ba, har mutane su dauke shi abin izgili, shi yasa yace:
“Ku sakawa ‘ya’yanku sunayen Annabawa, kuma mafi kyawun sunan da Allah yafi so shine, Abdullahi da Abdurrahman, sannan kuma sunan da yafi kowanne gaskiya shine: Haris da Hammam, mafi muninshi kuma shine, Harbu da Murrah.” [Abu Dawud]
Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya kara umartar iyaye da yin yanka yayin haihuwa, domin su nuna farin ciki ga Allah madaukakin sarki, yace:
“Duk wanda ya samu karuwa ta haihuwa, kuma yaso yayi yanka, to ya yanka wa namiji akuya sa’anni guda biyu, sannan kuma ‘ya mace akuya guda daya.” [Abu Dawud]
Saboda ma muhimmancinsa ne yasa al’ummah gaba daya take taya iyayen yaro murnar samun karuwa ta haihuwa.
Ayoyi da dama sun zo cikin Alkur’ani wadanda suke tabbatar da hakkokin yara, wurin shayarwa, Allah (SWT) yace:
“Kuma masu haihuwa (wadanda mazajensu suka sake su) suna shayar da abin haihuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda yayi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alheri.” [Bakarah: 233]
Ita shayarwa abu ce wadda tasirinta yake a bayyane wurin habakar jiki da tausayi da kuma nishadi na yaro, saboda mahimmancin kulawa da hakkokin yaro Annabi Muhammad (SAW) yayi umarni da yin adalci tsakanin ‘ya’ya wurin kyauta, a inda yace:
“Ku yi adalci tsakanin ‘ya’yanku wurin kyauta.” [Bukhari]
Hakanan kuma Annabi Muhammad (SAW) ya kasance yana yi wa iyaye nasiha da cewa:
“Kada ku rika yi wa ‘ya’yanku mummunar addu’a.” [Muslim]
Saboda idan aka amsa wannan addu’ar, to za ta iya zama sanadiyar tabewar yaro da lalacewarsa tsawon rayuwarsa, sai a wayi gari ya zama dan bindiga ko dan ta’addar da zai rinka muzgunawa al’ummarsa ta bangarori daban-daban!
Kamar yadda kuma addinin Musulunci ya bai wa yaro hakkoki da dama tun daga haihuwarsa, kamar cin gado, ko kyauta ko wakafi da dai sauransu.
Duk wadannan hakkokin na yaro suna tabbata ne a kanshi daga zarar an haifeshi, domin haka ne ma Annabi Muhammad (SAW) yace:
“Idan jinjiri yayi kuka, ko yayi kara, ko yayi atishawa (bayan an haife shi) to ya cancanci gado.” [Abu Dawud]
Bugu da kari, Annabi Muhammad (SAW) ya kwadaitar da a kyautata wa yara, da yi masu rahama, wato tausaya masu, da shigar masu da farin ciki, kamar yadda muka fahimta a mu’malolinsa da yara (SAW). Hakanan kuma ya kwadaitar da kulawa da su a ilmance da kuma a ibadance da kuma girmama yaro da karfafashi akan yin gaskiya da zaba masa abokai nagari, da yi masa addu’a da kuma kulawa da dabi’unsa. Da wadannan abubuwan ne yaro zai taso na gari abin yabo cikin al’ummah. Duk lokacin da al’ummah ta wofintar da yaran ta, ta wulakanta matasan ta, tayi sakaci da samarin ta, aka bar su babu ilimi, babu aikin yi, aka bar su kara-zube babu alkibla, to wallahi duk duniya ban ga mai iya hanasu su zama ‘yan bindiga ko su zama ‘yan ta’addar da za suci gaba da damun al’ummar su!
Wannan, a gaskiyar magana, shine ya jawo muna wannan bala’i da muke ciki a yau. Sakamako ne na sakacin mu!
Da wannan ne Khalifah Umar Dan Khattab ya kasance yana tafiya tare da Dan sa Abdullahi zuwa majlisin Annabi Muhammad (SAW), saboda ya koyi ilimi da ladabi da kuma girmama manya, da girmama jama’arsa da sanin muhimmancin kasar sa da sanin kimar dan Adam. Ga abin da Abdullahi Dan Umar (RA) yake cewa:
“Wata rana Manzon Allah (SAW) yace da Sahabbai: “A cikin bishiyoyi akwai wata bishiya wadda ganyenta ba ya faduwa, kuma tayi kama da Musulmi, wace bishiya ce wannan?” Abdullahi Dan Umar yace: “Sai mutane suka yi ta tunanin bishiyoyin daji daban-daban, sai ni kuma a raina na yi tunanin cewa ai wannan bishiyar dabino ce, amma sai naji kunyar na fadi amsar, sai Sahabbai suka ce: ya Manzon Allah ka fada muna ita, mun baka gari. Sai yace: “Ita ce bishiyar dabino.” Abdullahi yace: sai na fadawa babana cewa ita nayi tunani a raina tun farko”, sai yace: “Hakika da ka fade ta da yafi burge ni fiye da ace ina da kaza da kaza!” [Bukhari]
Hakanan ya zama wajibi a koya wa yara dabi’u da al’adu irin na addinin Musulunci, da kuma al’adun al’ummarsu saboda su rayu rayuwa mai nagarta a cikin al’ummah.
Akwai labarin yaron nan Amru Ibn Abi Salamah wanda ya taso tare da Annabi (SAW) a gidansa yake cewa:
“Na kasance yaro a gidan Annabi (SAW) alhali hannuna yana yawo cikin farantin abinci, sai yace da ni: “Ya kai wannan yaro, ka ambaci sunan Allah, kuma ka ci da damanka, sannan ka rika cin na gabanka.” Amru ya kara da cewa: “ban gushe akan wannan abu da Annabi (SAW) ya dora ni akai ba duk lokacin da zan ci abinci.” [Bukhari]
Ya ku jama’ah, Annabi Muhammad (SAW) kenan, gwarzon jagora, shugaba nagari, wanda yake zama tare da yara da matasa a koda yaushe, wadanda kowa yasan cewa sune manyan gobe, ya koya masu halaye da ladubba cikin tausayi da rahama. Annabi Muhammad (SAW) bai zamo mai gudun yara ba, bai zamo mai kyamar matasa ba. Bai zamo mai handame komai da komai ba shi kadai, daga shi sai ‘ya ‘yansa, ya bar matasa suna hamma ba. Ya jawo su a jika, ya taimake su. Ya dora su akan tafarki nagari, sai aka wayi gari sun zamo mutanen kirki, masu kishin al’ummarsu, masu kaunar kasar su, kuma masu bayar da kariya ga kasar su!
Amma a yau, akasin haka muke gani, shi yasa aka samar da wasu irin matasa masu yakar al’ummar su! Masu jin haushin kasar su da manyan su! Suna ganin cewa tun da kowa ya guje su, tun da kasar su bata kaunar su, to bari su zama ‘yan ta’adda, bari su shiga cikin gungun ‘yan bindiga, su tayar wa da kowa hankali, su addabi kasar su!
Ya ku ‘yan uwana masu daraja, ku sani, addinin Musulunci yazo da wata irin alaka mai girma tsakanin uba da ‘ya’yansa da jikokinsa, wannan alaka ita ce alakar kauna, soyayya da jinkai da tausayi da bayar da kulawa ta musamman ga wadannan ‘ya’ya a cikin dukkanin fannonin rayuwarsu. Uba shine matattarar ‘ya’yanshi a kowane lokaci, don haka ne ma Alkur’ani mai girma ya tabbatar da wannan alaka tare da zurfafa ta, musamman idan muka dubi kissar Lukman, na kiran da yake yiwa dansa, a inda yake cewa:
“Kuma a lokacin da Lukman yace wa dansa, alhali kuwa yana yi masa wa’azi, “Ya karamin dana! Kada ka yi shirka game da Allah. Lalle shirka wani zalunci ne mai girma.” [Suratu Lukman, 13]
Sannan idan kuma muka dubi irin alakar da ke tsakanin uba da ‘yar sa, za mu gani a cikin irin alakar da ke tsakanin Manzon Allah (SAW) da ‘yar sa Nana Fatimah (RA), kamar yadda Nana Aisha (RA) ta ruwaito cewa:
“Wata rana Nana Fatimah (RA) ta zo wurin Manzon Allah (SAW) tana tafiya irin tafiyarsa, sai yace mata: “Marhaban da ‘ya ta!” Sannan ya tsugunar da ita a gefensa na dama da na hagu, sannan ya rada mata wata magana sai ta fashe da kuka sai nace mata: “Don me kike kuka?” Sai Manzon Allah (SAW) ya sake fada mata wata maganar, sai ta kama dariya, sai nace: “ban taba ganin rana irin wannan ba, bakin ciki a tare da farin ciki?!” Sai na tambaye ta game da abin da ya fada ma ta, sai tace: “Ba zan iya fadar sirrin Manzon Allah (SAW) ba.” Bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) sai na tambaye ta, sai tace abin da ya rada mani shine; “Mala’ika Jibrilu yana yi mani tilawar Alkur’ani duk shekara sau daya ne, amma a wannan shekarar ya karanta mani sau biyu, to abin da na fahimta game da hakan shine ajalina ne ya kusanto, kuma ke ce farkon wadda za ta riske ni a cikin iyalan gidana.” Wannan ya sanya nayi kuka, sai ya sake cewa da ni: “Shin ba za ki yarda ba ki zama shugabar matan gidan Aljannah ko kuma shugabar matan muminai ba?” Sai wannan ya sa ni dariya da farin ciki.” [Bukhari]
Wannan shine misalin tarbiyyar Manzon Allah (SAW) game da ‘yar sa. Wato tarbiyya mai cike da tausayi da soyayya da kauna da rahama.
A yayin da dan Annabi (SAW) Ibrahim, kuwa yazo rasuwa, tausayinsa da jinkansa (SAW) sun fito fili, in da yake ce masa: “Ya Ibrahim, ba don wannan al’amarin gaskiya bane, kuma alkawarin tabbas bane, kuma rana ce mai hada mutane, ba don lokaci bane kididdigagge, da mun yi bakin ciki a kanka mai tsananin yawa sama da wannan, mu kam muna bakin ciki akan rabuwa da kai, hawaye na zuba, zuciya na bakin ciki, amma babu abin da zamu iya fada wanda zai fusata Allah (SWT).” Yayin da ya riga ya rasu, sai yace: “Kada ku sanya shi a likkafaninshi har sai na kalleshi.” Sai yazo ya rungume shi yana kuka.” [Muslim]
Kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake bai wa jikokinshi muhimmanci, da zabar masu mafi kyawon sunaye. Aliyu (RA) ya ruwaito cewa lokacin da ya samu karuwar Hassan, Manzon Allah (SAW) ya shigo yace ku nuna mani da na da aka samu karuwarsa, wane suna aka sa masa? Sai yace na sanya masa suna “Harbu”! sai Manzon Allah (SAW) yace: “Haba dai, ai sunansa Hasan.” Hakanan da aka haifi Husaini (RA), sai Manzon Allah (SAW) yace ku nuna mini da na, menene sunansa? Sai Aliyu yace na sanya masa suna “Harbu”! sai Manzon Allah (SAW) yace a sanya masa suna Husaini.” Da ya samu wani dan sai ya sanya masa suna “Harbu”! Sai Manzon Allah (SAW) yace: “Me aka sanya ma da na?” Sai yace: “Harbu” sai yace “haba dai, a sanya masa Muhsin”, yace: “Na radawa ‘ya’yana irin radin da harun ya yiwa ‘ya’yansa, ya sanya masu “Shabr” da “Shubair” da “Mushbir.” [Ahmad]
Yana daga cikin abin da ke nuni ga tsananin kaunar Annabi (SAW) ga jikokinsa, abin da Abdullahi dan Buraidah (RA) ya ruwaito daga babansa cewa:
“Naga Manzon Allah (SAW) wata rana yana huduba, sai ga Hasan da Husaini (RA) sun shigo, alhali akwai riguna jajaye akansu, suna fadi tashi irin na yara, sai Manzon Allah (SAW) ya sauka daga kan mimbari ya dauko su ya dora su kan cinyarsa, yace: “Allah yayi gaskiya a inda yake cewa: “Hakika dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne” [Suratuh Taghabun, 15], ga shi naga wadannan amma ban iya yin hakuri ba.” [Abu Dawud] sai yaci gaba da hudubarsa.
Haka nan dai kaunarshi take ga sauran ‘ya’yanshi. Wata rana ya kasance yana Sallah, alhali jikar shi Umamah ‘yar Zainab tana hannunshi, idan yayi sujada sai ya sauke ta, idan ya mike sai ya dauke ta. [Bukhari]
Wata rana Manzon Allah (SAW) ya fito Sallar azahar ko la’asar yana dauke da daya daga cikin jikokinsa Al-hasan ko Al-husain (RA), sai ya dora shi a gefen kafarsa ta dama sannan yayi Sujadah, ya jima bai dago ba. Sai babana yace: sai na daga kaina tsakanin mutane, sai naga ashe yaron ne ya hau bayan Manzon Allah (SAW) a lokacin da yayi Sujadah, sai na koma Sujadah ta, bayan Manzon Allah (SAW) ya gama Sallah sai mutane suka ce: “Ya Manzon Allah, kayi Sujadah a Sallah irin wadda ba kasafai kake irinta ba, shin wannan umurni ne akayi maka, ko kuwa wahayi ne ake maka a lokacin (shi yasa ka dade baka dago ba)? Sai yace: “Duk ba haka bane, da na ne kawai ya hau gadon baya na, ni kuma bana son in dago in katse masa wasansa.” [Nasa’i]
Wannan irin matakai na kaunar yara, da kaunar ‘ya ‘ya, ba sabon abu ba ne a rayuwar Manzon Allah (SAW), a’a sifa ce tashi tabbatacciya wadda kuma bata canzawa, shi yasa Abu Hurairah ya ruwaito cewa:
“Wata rana Manzon Allah (SAW) ya sumbaci Al-hasan dan Aliyu (RA) alhali Al’akra’a dan Habis yana zaune a wurin, sai Al’akra’a yace, lallai ni ina da ‘ya’ya goma, amma ban taba sumbatar ko daya daga cikinsu ba, sai Manzon Allah (SAW) yace: “Duk wanda baya jinkai to ba za’a jikanshi ba.” [Bukhari]
Duk da irin wannan kauna da soyayya da Manzon Allah (SAW) yake yi wa ‘ya’yansa da jikokinsa, hakan bai taba sanya shi zaluntar wani mutum daga cikin mutane ba saboda su. An ruwaito cewa Aliyu dan Abi Dalib (RA) ya shiga wurin Fatimah (RA) sai yace: “Hakika kirjina yana ciwo kwarai saboda aiki mai nauyi da nake yi, sai ita ma tace: “Ni ma ina fama da hannu saboda nika da nake yi.” Sai yace ma ta: “Ki tafi wurin Manzon Allah (SAW) ki nemi agaji da taimako, domin an kawo masa bayi, la’alla ya baki mai hidima daga ciki.” Sai ta tafi wurin Manzon Allah (SAW) ta fada masa kokenta. Sai Manzon Allah (SAW) yazo gida ya same su ita da Ali (RA) yace: “Ku kun zo wurina domin in baku mai hidima, ni kuma zan baku abin da yake shine mafi alheri a gare ku fiye da mai hidima, shine kuyi Tasbihi ga Allah bayan kowace Sallah sau talatin da uku, kuyi Hamdala sau talatin da uku, kuyi Kabbara sau talatin da hudu, idan kuma kunzo kwanciya bacci kuyi hakan, wannan guda dari kenan.” [Bukhari]
‘Yan uwa masu daraja, haka dai alakar uba take da ‘ya’yansa da jikokinsa, alaka ce wadda ta ginu akan soyayya da kauna. Madalla da irin wannan kauna da ke tsakanin fiyayyen halitta (SAW) da ‘ya’yansa da jikokinsa.
Yanzu ya ku jama’ah sai mu duba, kuma muyi tunani, kuma muyi wa kawunan mu adalci, yanzu irin wannan kauna da soyayya da Allah ya sanya tsakanin iyaye da ‘ya ‘yansu da kuma jikokinsu, ka auna misali, da ace dan ka ko jikanka yana cikin yaran da wadannan ‘yan ta’adda suka sace a jihar Katsina, don Allah yaya zaka ji? A ina zaka sa kan ka? Shin hakalinka zai kwanta? Haba jama’ah, Allah yana kiran mu da mu zama adilai fa!
Mu tuna fa wadannan yara ‘ya ‘yan wasu ne kuma jikokin wasu ne! Kuma iyayensu suna kaunar su, kuma suna son su matuka. Don haka ya zama dole, tilas, wajibi hukumomi suyi duk mai yiyuwa wurin kwato su daga hannun wadannan jahilan ‘yan ta’adda!
Ya ku jama’ah, wallahi lokaci yayi da za’a dauki kwararan matakai don kubutar da kasar mu Najeriya daga halin da ta samu kan ta a ciki na ibtila’in rashin tsaro!
Idan kuma kun ki ji, to duk ranar da talakawa suka fusata, suka fara dira a kan ku, ku da iyalan ku, to za ku yi bayani! Idan kunne yaji, to gangar jiki ya tsira! Kuma ko kai malamin addini ne, idan talakawa suka fahimci ana hada kai da kai ana zaluntar su, to zaka gane kurenka. Domin sai wata rana an wayi gari kana kan mimbari, wallahi talakawa su jawo ka, ka rikito kasa. Domin sun gano cewa kai baka cikin malaman Allah da Mnazonsa, kawai sun gano cewa kai dan cuwa-cuwar malami ne, kuma mugu azzalumi!!!
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post