Yadda mahara suka yi garkuwa da dan majalisar Taraba

0

Wasu mahara dauke bindigogi sun yi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Taraba mai suna Bashir Bape.

Honorabul Bashir Bapedake ne yake wakiltar Nguroje a majalisar jihar.

Maharan sun yi garkuwa da Bape a gidansa dake garin Jalingo da misalin karfe daya na daren Talata.

“Maharan sun fatattaki masu gadin gidan bayan dan bata kashi da suka yi kafinnan suka samu damar kutsawa cikin dakin Bape suka yi waon gaba da shi.

Wasu makwabtan Bape sun shaida cewa masu garkuwan sundiro gidan Bape a kan babura.

Idan ba a manta ba a ranar 30 ga Disamba na 2017, an taba yin garkuwa da wani dan majalisar jihar sai dai kuma Allah bai sa zai tsira da rai ba, domin sai da aka biya kudin fansa sannan suka kashe shi suka aiko da gawar sa.

Share.

game da Author