Yadda mahara suka sace Amarya da Ango, suka Kashe kawun dan majalisa a Katsina

0

Dan majalisan dake wakiktan shiyyar Safana a majalisar Jihar Katsina,
Abduljalal Haruna, ya bayyana wa PREMIUM TIMES, yadda ‘yan bindiga suka kashe Kawun sa a Kauyen Rumka dake karamar hukumar Safana, jihar Katsina.

Honarabul Haruna ya ce kawunsa Ismaila Supa ya rasa ran sa ne bayan yayi wa maharan gaddamar ba zasu bisu cikin daji ba.

” Wannan abu da ke faruwa a yankunan mu sun wuce gona da iri matuka. Abin yayi tsananin gaske.

” A kullum sai an afka gari ko kauye an yi awon gaba da mutane. Ko a jiya sai da aka sace wasu kauyawa 13 amma kuma bakwai daga ciki sun arce daga wajen maharan. Wasu sun tsira da rauni a jikin su, yanzu haka suna asibiti ana duba su.

Bayan haka kafin su fice daga wannan gari, sai da suka sace wata Amarya da Angonta wanda duka-duka basu wuce sati daya da aure ba.

Share.

game da Author