A wata takarda da kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa jami’an tsaro dake sintiri a hanyar Abuja-Kaduna sun kazhe wasu barayin shanu da suka nemi tsallakawa da shanu masu yawa da suka sace a hannu wasu fulani makiya.
Aruwan ya ce an kai wa maharan harin kwantar bauna ne basu sani ba kuma Allah ya sa suka fada tarkon da aka dana musu wanda kafin su ankara an yi wujiwuji da su.
An kashe mutum takwas cikin su sannan an kashe wasu shanu cikin wadanda aka sato za a ketara da su.
Haka kuma a wani samamen na daban jami’an soji da ‘yan sanda sun samu nasarar kashe wani dan bindiga yayin da suke kokarin ketarawa da wasu shanu da suka sato a hanyar Kaduna-Abuja, sai dai kuma daya daga cikin wanda ya fallasu ga jami’an tsaro wanda jami’in sa kai ne bai tsira da ransa ba a batakashin da suka yi da ‘yan ta’ addan.
Discussion about this post