A wani mummunar hari da Boko Haram suka kai wasu kauyukan jihar Barno, sun kashe mutum uku da banka wa makarantu da sauran gine-gine wuta a kauyukan dake cikin karamar hukumar Hawul.
Kakakin Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Barno, Isa Gusau, ya tabbatar da cewa Boko Haram sun banka wa makarantu wuta, haka sun banka wa wuraren ibada da wasu gine-gine da dama a cikin kauyuka hudu da ke karkashin Karamar Hukumar Hawul a Jihar Barno.
Kauyukan guda hudu sun hada Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da kuma Debro.
An kai masu wannan mummunan hare-hare a anar Asabar da dare.
“Sun kashe mutum uku a kauyen Shafa, cikin su akwai maharba biyu da wani farar hula daya. Sun kuma kwashe dubban buhunan amfanin gona, wadanda ba a dade da girbewa a gona aka kai gida ba. Sannan kuma sun rika kwashe kayan da ke cikin kantinan kauyukan karkaf.
Ya ce Zulum ya hau helikwafta, ya garzaya yankunan hudu duk ya ga irin barnar da aka yi masu.
Tuni dai Gwamna Babagana Zulum ya bar abin da ya ke yi a Abuja, ya garzaya Maiduguri domin gane wa idon sa irin barnar da Boko Haram su ka yi a kauyukan.
“Zulum ya je Yimirshik, Azare, Sabon-Kasuwa da kuma Shafa.” Inji Gusau.
Gwamna Zulum ya bada umarnin a gaggauta sake gyara makarantu, kantina da sauran wuraren da Boko Haram su ka lalata a kauyukan.
Sannan kuma ya umarci a kara wa jami’an tsaro masu sintiri a yankin Shafa motocin sintiri guda biyar.
Mataimakin Gwamna Umar Hawul ne ya raka Zullum zuwa Karamar Hukumar Hawul din, inda Boko Haram su ka yi wannan mummunar barna.
Akwai kuma Sanata Ali Ndume da wasu kwamishinoni guda biyu da su ka raka Zulum wannan ziyarar gaggawa.