1 – Tsakanin Gwamnatin Ganduje da Sani Danja
A watan Faburairun 2020, jarumin Kannywood, Sani Danja ya zargi gwamnatin Kano da garkame masa shagon daukan hotuna da bidiyo a Kano Saboda yana dan jam’iyyar PDP.
Danja yace saboda shi dan PDP ne gwamnati ta yi masa haka.
2 – Tsakanin Maryam Booth da Rufai Deezel
A watan Maris din 2020, jaruma Maryam Booth ta maka mawaki Ibrahim Rufai Deezell a Kotu saboda zargin fidda wata bidiyo nata dake nuna tsiraicin ta a yanar gizo.
Maryam ta ce ba tun yanzu ba Deezell ya rika yi mata barazanar yada wannan bidiyo yana neman ta bashi kudi ko ya yada.
” Ranar 27 ga watan Fabrairu a dakin Otel din Nanet dake Abuja ya dauki bidiyo batare da sanina ba.
” Na ce masa lallai ya goge wannan bidiyo.
” Amma ba tare da sanina ba sai ya yi kaman ya goge, ashe aika wa wani abokinsa yayi mai suna Ruky Haske.
” Tun daga nan ya fara yi min barazanar sai ya sami bidiyon don ya bata ni ko kuma in ba shi kudo masu yawa.
Shima Deezell ya shigar da kara Kotu yana kalubalantar zargin da Maryam take masa.
2 – Adam Zango ya wake Korona
Jarumin Kannywood, Adam Zango ya saki wata sabuwra wakar Korona , a watan May. Wammam Waka ta samu karbuwa matuka musamman a dalilin zaman gida da aka yi a dalilin Korona.
3 – Rasuwar mahaifin Ali Nuhu
A watan Yuni, Jarumi Ali Nuhu ya rasa mahaifinsa, Nuhu Poloma a jihar Gombe.
Mahaifin Jarumin, Malam Nuhu ya rasu a wani asibiti a garin Gombe bayan fama da yayi da rashin lafiya.
4 – Rasuwar Jaruma Fadila Mohammed
A watan August, jim kadan bayan rasuwar mahaifin Ali Nuhu, Jarumar Kannywood, Fadila Mohammed ita ma ta riga mu gidan gaskiya.
Fadila ta rasu bayan ta yi fama da rashin lafiya a Kaduna.
5 – Jack-Rich ya tallafawa Kannywood na gudunmawar naira miliyan 600
Wani attajiri mai suna Jack-Rich ya tallafa wa farfajiyar Kannywood da tallafin naira miliyan 600 domin raya farfajiyar.
6 – El-Rufai ya tallafa wa Kannywood da Fili da kuma gudunmawar kudin gini
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya tallafa wa Kannywood da da makeken fili da kuma gudunmawar naira miliyan 100 a lokacin da zasu gina wannan fili.
7 – Yadda rigar Rahama Sadau ya tada jijiyoyin wuya a farfajiyar Kannywood
A shekarar 2020 ne yan Najeriya musamman mazauna yankin Arewa, da yan Kannywood suka tofa bakunan su da yin tir da jaruma Rahama Sadau, bayan ta saka wani kaya da ya ja wani ya yi wa Annabi SAW izgilanci.
Daga karshe Rahama ta roki gafarar mutane da abokan aikin ta.
8 – Mawakiya Di’ja ta fito a fil din mati a zazzau, wanda shirine na Jaruma Rahama Sadau.
10 – Zaharaddeen Sani ya saka kare a fim din sa wanda shi Karen ne jarumin fim din.