Wadanda su ka arce da daliban sakandare a garin Kankara na cikin Jihar Katsina, su na magana da Gwamnatin Najeriya. Haka dai Gwamna Aminu Masari na Jihar ta Katsina ya bayyana a ranar Litinin.
Dama kuma a ranar Litinin din ce Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi karin bayanai daga Masari dangane da halin da ake ciki akan sace daliban na makarantar sakandare ta kwana, ta kimiyya, GSSS Kankara.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga gayya guda su ka darkaki garin Kankara wajen 11 na dare a ranar Juma’a, 11 Ga Disamba, su ka kutsa makarantar.
Har yau Buhari bai kai ziyara garin Kankara ba, duk kuwa da cewa ya na cikin jihar aka sace yaran.
Ministan Tsaro Bashir Salihi-Magashi ya yi alkwarin kwato yaran cikin kankanin lokaci.
Yayin da aka shiga kwanaki uku da sace yaran, Shugaba Buhari na ci gaba shan caccaka ganin cewa ya kasa kai ziyara makarantar da kuma garin na Kankara, ganin cewa ya na Daura kwance a cikin dare aka sace yaran.
Caccakar da ya ke sha ta kara kaimi ganin a ranar Litinin, ranar da Buhari ya rika kwanaki uku a Daura, ya ziyarci garken shanun sa.
Wannan ya kara ba jama’a mamaki, haushi da takaici, har wasu na cewa Buhari ya fi ganin darajar dabbobi da rayukan ‘yan uwan sa Katsina da ke hannun masu garkuwa da jama’a.
Dama ana jin haushin haushin yadda Buhari ya ki kai ziyara Barno, bayan da Boko Haram su ka yi wa ‘yan kwadago a gonar shinkafa yankan-rago, a Zabarmari, har matasa 43.