TURA TA KAI BANGO: Jama’a za su kaurace wa sayen kayan kyale-kyale masu tsada a cikin 2021- CBN

0

Karin maganar nan da Bauhaushe ke cewa ‘kowa ya ji zafin wuta, shi ke kara matsawa’ dai ta samu gindin zama a Najeriya, domin hasashe da kintacen Babban Bankin Najeriya CBN ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar cikin 2021 ‘yan Najeriya za su kauce wa sayen kaya masu tsada da kayan kyale-kyalen da ba na tilas a rayuwa ba.

Irin wadannan kayayyakin da CBN ya ce jama’a za su taka wa burki daga saye bagatatan sun hada da gidaje, motocin alfarma da duk wasu kayan kyale-kyale da masu tsadar da idan mutum ya saya, sai yi a jikin sa.

Rahoton Binciken Kayayyakin Amfani na CES a watanni ukun karshen 2020 ya nuna cewa an yi bincike a gidaje 2,070 da aka tabbatar da hakan.

Dama kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta fahimci tun bayan barkewar cutar korona a watan Maris, da kulle jama’a da aka yi cikin watan Afrilu, yawancin masu kallon tashoshin DSTV sun daina, sun koma su na kallo ta tashar GoTV.

Irin wannan kuma na nuna cewa a halin da ake ciki na sawun gida ya take na rakumi, babu wata fa’ida mutum ya kwashi dan abin da ya kamata ya yi tattali ya sayi gida ko mota da kudaden.

Da wahala a tambayi mutum ko a ji yana cigiyar gidan saye. Sannan kuma yawan tallar gidajen sayarwar da ake yi, ya nuna su kan su masu gidajen su ka bukatar kudi daga mai saye, amma ana neman mai sayen an rasa.

“Wadanda aka ji ra’ayin su, sun bayyana wannan dalili da matsin tattalin arziki, sai kuma raguwar kudaden shiga ga magidanta da karin nauyin iyali da ke hawa kan maigida.

Tattalin arzikin Najeriya na yi wa jama’a hannun-ka-mai-sanda cewa shekarar 2021 ba shekarar bushasha ba ce, shekara ce ta tattalin abin da ya shigo aljihu.

Bugu da kari ga shi kuma har yanzu ana tinjan-tinjan da matsalar aikin yi ga kuma alamomin sake barkewar korona zango na biyu a ake fama da shi a duniya baki daya, har da Najeriya.

Dama Bahaushe ya ce ‘idan duka ya yi yawa, na ka kadai ake iya karewa.’

Share.

game da Author