Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bayyana gaban majalisar Kasa ranar Alhamis domin yin jawabi kan matsalar tsaro da yaki ci yaki cinyewa a kasa Najeriya.
Idan ba a manta ba, tun a makon jiya
Shugaban majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamilla, ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai bayyana gaban ƴan majalisan domin amsa tambayoyin su kan tsaron kasa.
Dama kuma tun bayan kisan gillar da aka yi wa wasu manoma a Zabarmari, ƴan majalisar tarayya suka aika wa shugaban gaba Buhari sammacin ya bayyana a gabata domin amsa tambayoyi kan matsalar tsaro da ya addabi Najeriya.
A wancan lokaci Gbajabiamilla ya ce bada dadewa ba za a sanar da ranar da Shugaba Buhari zai bayyana a gaban majalisar.
” Mun ziyarci Buhari ne domin mu gaya masa halin da kasa ke ciki musamman game da tsaron kasa, sannan kuma da sakon ƴan majalisa na ya bayyana a gaban su domin qmsa tambayoyi game da tabarbarewar tsaro da kasar nan ta fada ciki.
Majalisar tarayya ta aika wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da sammaci ya gaggauta bayyana a gabanta.
Gaba dayan su ƴan majalisan sun amince Buhari ya bayyana a gaban majalisar domin ya amsa tambayoyi musamman game da tsaro da kisan gillar da aka yi wa manoma a Zabarmari.
Dan majalisa Satomi Ahmed ya mika wata kudirin gaggawa a gaban ƴan majalisar kan kisan gillar da aka yi wa wasu manoman shinkafa 40 a garin Zabarmari, jihar Barno.
Yadda Boko Haram suka kashe manoman shinkafa 44 a jihar Barno
Akalla manoman shinkafa sama da 40 wasu mahara da ake zaton Boko Haram ne suka yi wa kisan gilla a tsakiyar gonakinsu a daidai suna aikin girbi.
Dan majalisar Tarayya dake wakiltar yankin Ahmed Satomi, da aka kai wa hari ya shaida haka yana mai cewa zuwa yanzu an mika musu gawarwakin manoma 44 da aka yi wa kisan gilla a gonakin su, wanda za a rufe ranar Lahadi.
” Manoma da masu kamun kifi 44 da aka kawo mana gawarsu zuwa yanzu. Duka wadannan manoma na aiki ne a wani katafaren gonan shinkafa da ke garin Garin-Kwashebe.
An yi jana’izan mamatan ranar Lahadi a Zabarmari.
Haka kuma suma a majalisar Dattawa, sanatoci kira suka yi da shugaba Buhari ya tsige manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar nan.
Shugaba Buhari zai yi jawabi ga ƴan majalisan ranar Alhamis, kamar yadda majiya kwakkwara ta sanar wa PREMIUM TIMES da can cikin fadar shugaban kasa.