TINUBU A BARNO: Kada a bari Kashe-kashen nan su ci gaba fa

0

Tsohon Gwamnan Lagos, kuma jigon jam’iyyar APC, Bola TinubBarno. bayyana cewa kashe-kashen da ke faruwa na neman shan kan Najeriya, don haka ya zama tilas kada a bari su hadiye kasar baki daya.

Tinubu ya je Barno ne domin yi wa Gwamnati da al’ummar jihar ta’aziyya, jaje da taya su alhini da jimamin kisan da Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa su 43 a kauyen Zabarmari da ke cikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Barno.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Barno da ke Maiduguri, babban birnin jihar, Tinubu ya ce babu yadda za a iya samun zaman lafiya da ci gaba a cikin kasar da Kashe-kashen rashin imani yq zama ruwan dare a cikin ta.

“Ba za mu iya samun ci gaba ba a kasar da ake yi wa talakawa yankan-rago a inda su ke neman abincin su.” Inji Tinubu.

Tinubu wanda tun da farko ya kai wa Gwamna ziyarar ta’aziyya, ya ce ya kamata a hanzarta tun kafin wuri ya kure a rika jawo yara matasa ana horar da su wajen hanyoyin bunkasa su, maimakon a rika barin su na bin baudadden tafarki.

An tqmbaye shi dangane da markabun da ake yi cikin jam’iyyar APC. Sai ya ce ai ya je Barno ne domin yin ta’aziyya, alhini da jimamin asarar rayukan da aka yi.

Bayan ya bar Gidan Gwamnatin Barno, Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya a Fadar Shehun Barno

Share.

game da Author