Tattalin Arziki: Buhari ya yaba da irin juriyar ‘yan Najeriya, ya ce a koma amfani da gas, a rabu da fetur

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa irin juriyar rayuwar kuncin da ‘yan Najeriya ke hakurin zama ciki. Ya na mai cewa ana nan ana ta kokarin lalubo bakin zaren yadda za a magance matsalolin tattalin arziki.

Da ya ke magana ranar Talata a Abuja, Buhari ya kuma yaba wa kungiyoyin kwadago, saboda dattako da fahimtar halin da ake ciki da su ka yi.

Buhari ya yi bayanan ne a lokacin bude Shirin Amfani da Gas Gadan-gadan a Abuja, inda ya ke magana kai-tsaye daga Ofishin sa.

“Bari na jinjina wa ‘yan Najeriya dangane da irin zaman juriyar da su ke nunawa. Tare da yaba wa gamayyar kungiyoyin kwadago, saboda dattako, fahimta da kuma kishin da su ka nuna. Saboda haka Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen kokarin shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arziki.”

Daga nan sai Buhari ya shawarci ‘yan Najeriya su rungumi tafarkin amfani da gas, a matsayin sauki fiye da fetur.

Ya ce wannan shiri na bunkasa harkokin gas ya zo a daidai, musamman tanin yadda farashin danyen man fetur ke yin faduwar-‘yan-bori a kasuwannin mai na duniya.

“Wannan tsari zai magance matsalolin da ake fuskanta bayan cire tallafin fetur da gwamnati ta yi. Sannan kuma bunkasa bangaren gas zai kara samar da ayyukan yi ga dimbin ‘yan Najeriya.”

Buhari ya ce shirin maida motoci amfani da gas abu ne muhimmi da zai saukaka al’amurra da kunkasa tattalin arziki ta fannin gas, ganin yadda harkar fetur ta koma jula-jula a kasuwannin duniya.

Share.

game da Author