Akalla mutum 3,656 ne cutar korona ta kashe a ranar Laraba, 16.9 Ga Disamba a Amurka, yayin da mutum 247,403 su ka kamu da cutar duk a ranar ta Laraba.
Cibiyar Bincike da Tantancewa ta cikin Jami’ar Johns Hopkins (JHU) da ke Baltimore ce ta fitar da lissafin adadin mamatan da wadanda su ka kamu.
Ta fitar da bayanan safiyar Alhamis, 17 Ga Disamba
Wannan ya kawo adadin wadanda su ka kamu da cutar a kasar mai al’umma milyan 330, zuwa mutum milyan
Wannan ne adadi mafi yawa da muni na mamata da wadanda sub ka kamu a kullum, tun bayan mutum 233,133 da su ka kamu ranar Juma’a 11 Ga Disamba, inda kuma a ranar mutum 3,306 ne su ka mutu.
Gaba daya dai an tabbatar da kamuwar mutum milyan 19.9 gaba dayan kasar mai al’umma milyan 330.
Tun bayan barkewar cutar dai sama da mutum 307,500 ne ta kashe a Amurka, watau ta kashe fiye da kisan da ta yi a wata kasa kenan a duniya.
Shafin intanet na Jami’ar Johns Hopkins University da ke birnin Baltimore dai ya na kara bibiyar shafin sa a ko yaushe. Kuma har ma adadin da jami’ar ta bayyana, sun haura wadanda Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa.
Amurka ta samu kan ta cikin bala’in cutar korona tun daga farkon barkewar ta, lokacin da Shugaba Donald Trump ya ki daukar cutar da muhimmanci, ya mayar da ita abin barkwanci ga kasar Chana.
Sai kuma yawan gardandami da ya rika yi wa masana, musamman tankiyar da Ya rika jefa kan sa, tsakanin sa da masanin cututtuka na kasar, Anthony Pauci, ta haifar wa kasar gagarimar matsala.