Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa akalla mutum miliyan 8 ke mutuwa duk shekara daga cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin busa taba sigari a duniya.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya fadi haka ne a wata takarda da PREMIUM TIMES ta samu ranar Talata da ya gabata.
Ghebreyesus ya ce bullowar cutar Korona ya taimaka wajen rage yawan mutanen dake busa taba sigari a duniya.
“Duk shekara mutum miliyan 8 ne ke mutuwa a dalilin fama da cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin busa taba sigari. Ana sa ran cewa idan aka ci gaba da fadakar da mutane game da illolin ta za a samu raguwar masu mutuwa da daman gaske.
A shekarar 2017 WHO ta yi hasashen cewa rashin daukan matakan hana busa taba ka iya sa duniya ta samu karuwa a yawan mutanen da taba ke kashewa a duk shekara daga miliyan 6 zuwa miliyan 8.
Bayan shekara uku duniya ta samu karin mutum sama da miliyan 8.
Taba na daya daga cikin abubuwan dake haddasa cututtukan dake kama zunciya, ciwon siga, ciwon dake kama hakarkari, daji da sauran su.
Bincike ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ne ke mutuwa duk shekara daga cututtukan da ke kama zuciya a dalilin busa taba da ake yi.