Ta’addanci zai iya ci gaba da kasancewa a Najeriya har nan da shekaru 20 masu zuwa

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya ja wa kan sa caccaka da tir, bayan ya bayyana cewa ta’addanci da yakin sunkuru zai iya ci gaba da kasancewa a Najeriya har nan da shekaru 20 masu zuwa.

Duk da cewa Buratai da sauran manyan hafsoshin tsaron kasar nan sun haura shekarun yin ritayar su, ga shi kuma sun kasa kawo karshen ta”addanci, Buhari ya ki sallamar su, duk da korafin da akasarin ‘yan Najeriya ke yi.

A karo na uku kenan Majalisar Dattawa na yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige hafsoshin tsaron kasa.

Kira na baya-bayan nan sun yi shi a ranar Talata, bayan Boko Haram sun yi wa manoma 43 yankan rago a kauyen Zabarmari, cikin Jihar Barno.

Idan za a iya tunawa, farkon 2017 Buratai ya ce sun gama da Boko Haram, har ma ya kai wa Shugaba Buhari ganimar tutar Shekau da ya ce an tsinto bayan fasa babban sansanin Boko Haram da ke cikin Sambisa.

Sau biyu ana bayyana cewa har Shekau kan sa an kashe shi. Amma bayan kwanaki sai shugaban na Boko Haram ya fito ya na cika-baki kan sojojin Najeriya da gwamnatin kasar dungurugum.

Buratai ya yi furucin sa a ranar 1 Ga Disamba, a shafin sa na Facebook, inda ya bayyana cewa.

“Ya kamata jama’a su tantance tsakanin maharan sari-ka-noke da ‘yan ta’adda. Wannan kuwa ya danganta ta fuskar da mutum ya kalle su. Kafin a ce an ga bayan ta’addanci a kasar nan, za a iya kai nan da shekaru 20.

“Saboda haka wannan aiki ne na sojoji, sauran jami’an tsaro da al’umma baki daya.”

Furucin na Buratai ya janye masa Allah-wadai daga ko’ina a cikin kasar nan. Musamman ganin sa cewa ya yi shi a lokacin da Najeriya ke cikin halin gaba damisa baya siyaki.

Yayin da Boko Haram su ka hana zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas, masu garkuwa da mutane sun mamaye Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, har ma da wani yankin Arewa maso Gabas.

Share.

game da Author